Da Duminsa: INEC ta bayyana makudan biliyoyin da take nema don zaben 2023

Da Duminsa: INEC ta bayyana makudan biliyoyin da take nema don zaben 2023

  • Hukumar INEC ta bayyana adadin kudaden da take bukata domin aikin zabe mai zuwa na 2023 ciki har da na fidda gwani
  • Hukumar ta ce akalla tana bukatar Naira biliyan 305 domin gudanar ayyukan zaben har zuwa kammala shi
  • Sai dai, har yanzu akwai takardun da ke gaban shugaba Buhari kn yiyuwar yin kwaskwarima ga dokar zaben kasar

Abuja - Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar za ta bukaci Naira biliyan 305 domin gudanar da zabukan 2023.

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa a zauren majalisar a ranar Litinin 20 ga watan Disamba, 2021, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda ‘yan majalisun Najeriya suka karkatar da sama da Naira biliyan 5.2 a 2019

Shugaban INEC, Mahmud Yakubu
Babbar magana: INEC ta bayyana makudan biliyoyin da take nema don zaben 2023 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban na INEC ya kuma lura da cewa adadin kudin ne zai baiwa hukumar damar shirya zabe da kuma siyan duk kayan aikin zaben da ake bukata da kuma gudanar da zabukan fidda gwani a fadin kasar nan.

Sai dai ya bayyana cewa tuni hukumar ta karbi Naira biliyan 100 daga cikin kudaden da ake bukata na zaben.

A halin da ake ciki, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi Sanata Jibrin Barau, ya bayyana cewa za a gabatar da kasafin kudin shekarar 2022, a yi muhawara, sannan a zartar da shi agober Talata 21 ga watan Disamba.

Hakazalika, babu wani bayani kan ko shugaba Buhari ya rubuta ko mikawa majalisar dokokin kasar wasika kan matakin da ya dauka na bayarwa ko janye kudurin sa na yin kwaskwarima ga dokar zabe.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar tattali za ta sa rashin biyan haraji ya kai mutum kurkuku na tsawon shekara 5

Wa’adin kwanaki 30 da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade ga shugaban kasa ya mayar da martani kan kudirin ya kare ne a ranar Lahadi 19 ga watan Disamba, kamar yadda Independent ta tattaro.

A halin da ake ciki, majalisar dokokin kasar za ta shiga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara daga ranar Talata 21 ga watan Disamba.

Bayan cire shi cikin 'yan takara, dan takarar APC a Anambra ya magantu

A baya, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba, Sanata Andy Uba, ya yi watsi da hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya ya yanke wanda ya soke takararsa a matsayin dan takaran APC.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar yakin neman zaben Sanata Andy Uba (SAUGCO), Ikechukwu Emeka Onyia ya fitar, ya ce Andy Uba zai daukaka kara kan hukuncin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro

Daya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC, George Moghalu, ya maka Andy Uba da jam’iyyar a kotu yana kalubalantarsu kan magudi a zaben fidda gwani na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel