Rikicin jam'iyyar APC a jihar Kano ba zai raba mun hankali ba, Gwamna Ganduje

Rikicin jam'iyyar APC a jihar Kano ba zai raba mun hankali ba, Gwamna Ganduje

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yace rikicin APC dake faruwa a jiharsa bai isa ya ɗauke masa hankali daga aikin al'umma ba
  • Ganduje yace abinda ke faruwa tamkar al'ada ce ta mulkin demokaradiyya, domin ya saba faruwa a siyasance
  • Yace kwarewarsa a siyasa ta fi karfin ya tsaya wannan rikicin na ɗaga masa hankali, amma ya nuna bukatar zaman lafiya a APC

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yace rikicin jam'iyyar jam'iyyar APC a jihar ba zai ɗauke wa gwamnatinsa hankali daga kokarin inganta rayuwar al'ummarta ba.

Ganduje, a wata sanarwa da kakakin gwamnan, Abba Anwar, ya fitar, ya faɗi haka ne a gidan gwamnati dake Kano yayin taron masu ruwa da tsaki ranar Lahadi.

Dailytrust ta rahoto Ganduje na cewa kwarewarsa a siyasa ta fi ƙarfin wannan ƙaramin rikicin a APC ta Kano ya daga masa hankali kuma ya taba ayyukan gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Gwamna Ganduje
Rikicin jam'iyyar APC a jihar Kano ba zai raba mun hankali ba, Gwamna Ganduje Hoto: naijanews.com
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto Ganduje yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kamata kowa ya san cewa kwarewa da basirar mu a siyasa ba zai bar wannan ɗan ƙaramin rikicin ya raba mana hankali ba wajen kokarin kawo wa jihar mu cigaba."
"Abin da kuke ganin yana faruwa a jam'iyyar APC ta jihar mu al'ada ce ta demoƙaradiyya, ya saba faruwa ba wai sabon abu bane."

Wane taro tsagin Ganduje ya gudanar?

Gwamnan ya ƙara da cewa sun gudanar da wannan taron ne domin kara tattauna wa kan muhimmancin zaman lafiya a cikin jam'iyya.

"Ba zamu bari mu koma baya ba saboda rikicin jam'iyya wanda ya saba faruwa. Wannan rikicin ba wani abu bane a demokaradiyya."

Taron ya samu halartan Sanata Kabir Gaya, mambobin majalisar dokokin tarayya, kakaki da mambobin majalisar dokokin jihar Kano, shugabannin APC na ƙananan hukumomi, gunduma da kuma jiha.

Kara karanta wannan

Babu ɗan ta'addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan ya sha alwashi

A wani labarin na daban kuma An maka tsohon gwamna gaban kotu kan ya ƙi neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Wasu masu kishin ƙasa sun maka tsohon gwamnan Abia gaban kotu kan ya ƙi fitowa takarar shugaban ƙasa a 2023.

A cewarsu, suna bukatar kotu ta tilasta masa nuna sha'awar neman takara, domin shi kaɗai ya rage da zai iya ceto Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel