Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

  • Jagoran yan bindiga, wanda ake ganin ya addabi jihar Zamfara da wasu yankuna, Bello Turji, ya nemi a zauna zaman sulhu
  • A ciki wasikar da ya aike wa shugaba Buhari, gwamna Matawalle, da sarkin Shinkafi, Turji ya nemi a cika wasu sharuɗɗa 4
  • Daga ƙarshe ya nemi hukumomi kada su yaudare su, domin ba su rubuta wannan wasikar da yaudara ba

Zamfara - Sanannen ɗan bindigan nan da ya addabi wasu yankuna jihar Zamfara, Bello Turji, ya nemi a yi zaman sulhu domin kawo karshen kashe-kashe a yankunan jihar.

A wasikar da ya aike wa shugaban Buhari, gwamna Matawalle, da Sarkin Shinkafi, Turji, ya sha alwashin aje makamansa bisa wasu sharuɗɗa da ya gindaya.

A rahoton Aminiya Hausa ta samu kwafin wasikar mai shafi uku, ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, Matawalle

Legit.ng Hausa ta tattro muku abu hudu da ɗan ta'addan ya nemi a yi kafin ya aje makamai.

Wasikar sulhu
Muhimman abubuwa hudu da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

1. Gwamnati ta soke kungiyar yan sa'kai

A cewarsa matukar gwamnati ta rushe ƙungiyar yan sa'kai to da izinin Allah duk wani kashe-kashe da yan bindiga ke yi ya zo ƙarshe.

Haka nan kuma yace dole sai an cire ƙabilanci da ake nuna musu (wato fulani) a koma ƙasa ɗaya dunƙulalliyar kamar yadda take a baya.

2. Zaman sulhu da sarakuna da Malamai

Ƙazalika a wasikar sa, Turji, ya nemi masarautar Shinkafi ta shirya musu zama da sarakunan ƙasar nan da kuma manyan malamai domin tattaunawar adalci.

Ya yi alƙawarin matukar aka shirya wannan zama, to zai karbi duk wata bindiga da ake aikata ta'addanci da ita ya miƙa wa hukumomin gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Babu ɗan ta'addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan ya sha alwashi

Wani ɓangaren wasikar, yace:

"Idan haka ta samu (Zaman Sulhu) to ni Muhammad Bello Turji Kachalla, na yi alƙawarin zan karbi dukkan bindigun da ake aikata ta'addanci da su na miƙa wa gwamnatin Najeriya."

3. A daina hattarar mu a ko ina

Sanannen ɗan bindigan ya ƙara da tabbatarwa sarkin Shinkafi da gwamna Matawalle cewa su ba faɗa da gwamnati suke son yi ba, kuma ba wata ƙungiya suke yunkurin kafawa ba.

Ya bayyana cewa cin zarafin da ake wa Fulani yan uwansu a faɗin ƙasar nan da nuna musu bambanci shine ummul aba'isin wannan abubuwan na rashin zaman lafiya.

4. Muna bukatar ganin Sheikh Gumi

Abu na ƙarshe kamar yadda ya rubuta a wasikarsa, Turji yace yayin zaman sulhu suna bukatar a haɗa manyan sarakuna da manyan malaman ƙasar nan baki ɗaya, kuma suna bukatar ganin Sheikh Ahmad Abubakar Gumi.

Bugu da ƙari, yace sun san Sheikh Gumi, ya taba zuwa har inda suke ya musu waazi kuma wa'azinsa ya musu amfani, shiyasa suke son zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da bindigu

Daga ƙarshe Turji yace wannan ne dalilinsa na rubuta wannan wasiƙa kuma dagaske yake ba da yaudara ba, kamar yadda baya son a yaudare su.

A wani labarin na daban kuma gwamnan Kogi ya sha alwashin babu ɗan ta'addan da zai shiga jiharsa kuma ya fita da rayuwarsa

Ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na haɗa kai da dukkan hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar daga mutane masu tunanin aikata ta'addanci ba tare da tausayi ba.

Yace gwamnatinsa a shirye take ta ɗauki tsattsauran mataki kan bara gurbin dake shigowa jihar domin tada zaune tsaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel