Babu ɗan ta'addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan Arewa

Babu ɗan ta'addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan Arewa

  • Gwamna Yahaya Bello ya yi alƙawarin cewa duk wani ɗan ta'adda da ya shiga jihar Kogi ba zai fita da rayuwarsa ba
  • Yace gwamnatinsa a shirye take ta ɗauki tsattsauran mataki kan bara gurbin dake shigowa jihar domin tada zaune tsaye
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu yan fashin daji sun fara kai hare-hare yankunan ƙaramar hukumar Yagba West

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin ɗaukar tsattsauran mataki kan yaan ta'addan dake shigowa jiharsa domin tada hankulan mutane.

Dailytrust ra ruwaito gwamnan na cewa matukar suka shigo jihar, to babu makawa zasu gamu da ajalinsu.

Gwamna Bello ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi bakuncin shugaban ƙaramar hukumar Yagba West, Pius Kolawole, domin tattaunawa kan fashi da makami a yankinsa da kuma matakan da aka ɗauka.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Gwamna Yahaya Bello
Babu ɗan ta'addan da zai shigo jihata ya fita da rayuwarsa, Gwamnan Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na haɗa kai da dukkan hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar daga mutane masu tunanin aikata ta'addanci ba tare da tausayi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk wani ɗan ta'adda ba zai fita da rai ba - Bello

Yahaya Bello ya bayyana cewa babu wani ɗan ta'adda, da zai shigo jihar Kogi domin aikata ta'addancinsa, kuma ya fita a raye.

Tribune ta ruwaito Gwamnan yace:

"Idan yan ta'adda kamar 20 ne suka shigo jihar Kogi, to ko guda ɗaya ba zai fita da rayuwarsa ba."

Gwamna Bello yace har yanzun akwai burbushin masu aikata manyan laifuka a jihar, ya gargaɗi cewa duk wanda ya shiga hannu zai fuskanci fushin doka.

Hakanan kuma ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Yagba West bisa jajircewarsa da kuma kokarin da yake yi wajen shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, Matawalle

Wace nasara aka samu?

Tun da farko, shugaban ƙaramar hukumar, Pius Kolawole, ya shaida wa gwamnan cewa kokarin da ake cigaba da yi ya fara haifar da ɗa mai ido.

Yace jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka wasu da kuma kama wasu daga cikin yan fashin dajin da suka kai hari yankunan Egbe da Odo Ere a baya-bayan nan.

A wani labarin na daban kuma Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da makamai a Legas

Yayin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, jami'an kwastam sun yi babban nasarar dakile yunkurin shigo da makamai

Jami'an kwastam na Tin Can a Legas sun yi ram da wata kwantema makare da katan-katan na bindigu da aburusai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel