Ana wata ga wata: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na tsagin Ministan Buhari a Bauchi

Ana wata ga wata: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na tsagin Ministan Buhari a Bauchi

  • Wata kotu dake zamanta a jihar Bauchi, ta rushe shugabannin jam'iyyar APC na tsagin ministan ilimi, Adamu Adamu, a jihar Bauchi
  • Wannan dai ya biyo bayan ƙarar da wasu fusatattun mambobin jam'iyyar suka shigar bayan darewar APC gida biyu a Bauchi
  • Rahoto ya nuna cewa tun bayan kammala zaɓen shugabannin a ranar 16 ga Oktoba, mambobin APC suka ce ba su amince ba

Bauchi - Wata babbar kotu a jihar Bauchi, ta tsige shugaban jam'iyyar APC, Babayo Ali-Misau, da sauran shugabanni a matakin jihar Bauchi.

A ranar 16 ga watan Oktoba, babban taron jam'iyyar APC na jihar Bauchi ya fitar da Ali-Misau na tsagin ministan Ilimi, Adamu Adamu, a matsayin shugaba.

Sai dai rahoton Daily Nugerian ya nuna cewa tun a wancan lokacin mambobin APC sun yi watsi da shi, wanda yasa jam'iyyar ta dare gida biyu a jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri

Adamu Adamu
Ana wata ga wata: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na tsagin Ministan Buhari a Bauchi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wasu daga cikin fusatattun mambobin jam'iyyar, sun garzaya sun shigar da kara a gaban kotu, inda suka nemi a a rushe sabbin shugabannin saboda karya doka, da kuma ɗauki dora da wasu, "Yan siyasan Abuja" suka yi.

Me karar ta kunsa?

A wata takardan kotun da muka samu ranar Lahadi, karar wacce Mohammed Sherrif ya shigar, ta nemi a rushe shugabannin APC a matakin jiha na karkashin Ali-Misau.

Sauran waɗan da ke cikin karar sun haɗa da, shugaban rikon kwarya na APC ta ƙasa, gwamna Mala Buni, shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki na Bauchi, Adamu Adamu, Yakubu Dogara da wasu mutum 39.

Shin kotu ta yanke hukunci ne?

Da yake yanke hukuncin cikin shari'a, alkalin kotun, mai sharia Kunaza Hamidu, ya umarci shugabannin su daina bayyana kansu a matsayin shugabannin APC, yayin da lamarin ke gaban kuliya.

Kara karanta wannan

Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Tribune Online ta rahoto Wani sashin hukuncin kotun yace:

"Shugabannin da ake kara su daina nuna kansu a matsayin halastattun shugabannin APC a jihar Bauchi, yayin da lamarin ke gaban kotu ana cigaba da sauraron shari'a."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 16 da kansiloli a jihar Ekiti

Jam'iyyar APC mai mulki ta lashe baki ɗaya kujerun ciyamomi 35 da kansiloli 176 cikin 177 a zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar Ekiti ranar Asabar.

Tribune Online ta tattaro cewa zaben ya gudana a dukkan kananan hukumomi 16 da kuma yankuna 19, da gundumomi 177 dake faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel