Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri

Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri

  • Alamu na nuna cewa, Tinubu zai koma tsagin Shekarau a jihar Kano yayin da tsagin ke jagorantar APC a jihar
  • An ruwaito cewa, Shekarau ya gana da Tinubu a jihar Legas, inda ake kyautata zaton sun tattauna batutuwan siyasa ne
  • An samu tangarda tsakanin 'yan APC a jihar Kano, lamarin da ya haifar rikicin har da kone ofishin APC a jihar

Legas - Malam Ibrahim Shekarau, jagoran jam’iyyar APC a jihar Kano, ya gana da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam’iyya mai mulki na kasa a ranar Lahadi.

Taron wanda ya gudana yayin da rikicin ya dabaibaye jam’iyyar APC a Kano, ya gudana ne a Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Abdullahi Ganduje da Shekarau dai sun yi ta gwabza rikici domin ganin kowa ya jagoranci jam’iyyar a jihar Kano.

Tinubu da Shekarau
Rikicin APC a Kano: Da alamu Tinubu zai koma tsagin Shekarau, sun yi ganawar sirri | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Amma a makon da ya gabata, wata babbar kotun Abuja ta rushe tsagin Ganduje na APC tare da bayyana bangaren Shekarau a matsayin sahihi da aka amince dashi.

Mai shari’a Hamza Muazu, wanda ya yi shari'ar, ya kuma hana bangaren Ganduje nada sabon shugaban zartaswa.

Bayan yanke hukuncin, rikicin ya dauki wani sabon salo, yayin da Nureini Jimoh, babban Lauyan Najeriya wanda ya wakilci Shekarau, ya sha kulle a ofishinsa daga jami’an gwamnatin jihar Kano.

Jimoh da ma’aikatansa sun kasance a kulle na tsawon sa’o’i har sai da aka sake bude ginin daga baya.

Kwana daya bayan hukuncin, an kona ofishin yakin neman zaben gwamna na Sanata Barau Jibrin.

Duk da cewa tsagin Ganduje ya nisanta kansa da wannan lamari, bangaren Shekarau ya kai kara ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda, inda suka ce dole ne a kamo mutanen Ganduje.

Ganduje dai na hannun damar Tinubu ne kuma ya nuna goyon baya ga Tinubu don tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

A karon farko tun bayan fara taron shekara-shekara da ya fara shekaru 10, Tinubu ya yi na 2021 a Kano, matakin da wasu masana suka fassara a matsayin wani yunkurin tsayawa takara a 2023.

Ya kuma kai ziyara Kano da dama yayin da majalisar dokokin jihar da ke tsagin Ganduje ta yi alkawarin yin aiki da Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Batun zai iya canzawa

A hasashen Daily Trust, tunda a yanzu bangaren Shekarau na rike da madafun iko, mai yiwuwa Tinubu ya sauya domin neman dace a siyasance a jihar ta Kano mai yawan kuri'u.

Ganawar ta Shekarau da Tinubu an yi ta ne bayan gwamnonin APC guda biyu sun yi jawabi ga Ahmadu Danzago, shugaban tsagin Shekarau a APC a Kano.

Gwamna Kayode Fayemi (Ekiti) da Mohammed Baduru Abubakar (Jigawa) duk sun yi jawabi ga Dazango a matsayin shugaban jam’iyyar APC a wajen taron lacca na bikin cika shekaru 21 da kafa gidan Mambayya na Jami’ar Bayero da ke Kano.

Ganduje na cikin bakin da suka halarci taron.

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske kan dalilin da yasa ta garkame ginin ofishin Barista Nuraini Jimoh.

Daily Trust ta ruwaito yadda Jimoh, daya daga cikin lauyoyin Malam Ibrahim Shekarau da wasu ma'aikatansa aka garkamesu na tsayin sa'o'i a cikin ofishinsa bayan umarnin gwamnatin.

Lamarin ya auku ne bayan sa'o'i 24 da tsagin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na Shekarau ya lallasa Gwamna Abdullahi Ganduje a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel