Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

  • Babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Ondo ta samu gagarumin cigaba a jihar yayin da ake fuskantar babban zaɓen 2023
  • Mambobin jam'iyyar ADP karkashin jagorancin shugabansu, Prince Foluso Mayowa Adefemi, sun sauya sheka zuwa PDP
  • A cewar mutanen, lokaci ya yi da za'a haɗa karfi da karfe wajen kawo karshen mulkin jam'iyyar APC mara manufa a ƙasar nan

Ondo - Jaridar Leadership ta rahoto cewa kamanin mambobin jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) 10,000 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ondo.

Shugaban jam'iyyar, Prince Foluso Mayowa Adefemi, shine ya jagoranci mambobin daga faɗin kananan hukumomi 18 zuwa PDP.

A cewar waɗan da suka sauya shekan, lokaci ya yi da za'a fatattaki jam'iyyar APC daga madafun iko a kowane matakin gwamnati na ƙasar nan.

Jam'iyyar PDP
Mambobin jam'iyya sama da 10,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakanan kuma sun ƙara da ikirarin cewa yan Najeriya sun gaji haka nan da mulkin kama karya, wanda babu tsayyayyar manufa mai kyau a cikinsa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi magana kan shirin gwamna Umahi na sauya sheka zuwa PDP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan PDP ya karbi masu sauya shekan

Da yake jawabi a wurin tarban mambobin ADP, jagoran PDP a yankin kudu maso yamma, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, ya tabbatar wa mutanen suna da rawar takawa a PDP.

Makinde, wanda ya samu wakilcin ɗan takarar PDP a zaɓen gwamnan Ondo 2020, Eyitayo Jegede SAN, yace jam'iyyarsu a shirye take ta baiwa mutanen duk wata dama ba tare da nuna banbanci ba.

Bugu da kari ya shaidawa sabbin mambobin cewa babu hayaniya a jam'iyyar PDP, kuma akwai haɗin kai da jawo kowa a jiki.

Ƙun yi abinda ya dace- PDP

Tun da farko, shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo, Fatai Adams, ya yaba wa sabbin yan jam'iyya bisa ɗaukar matakin da ya dace.

Yace:

"Bangaren ilimi, tattalin arziki, ɓangaren lafiya da sauran manyan ɓangarorin ƙasar nan sun lalace karkashin wannan mulkin, kuma duk wani mai tunani dole ya damu sosai."

Kara karanta wannan

Tsagin adawa da Tinubu a Legas sun bar APC, Saraki ya karbe su zuwa PDP

A wani labarin kuma Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP

Jigon jam'iyyar hamayya PDP a jihar Abia, Dakta Nkole, ya gargaɗi PDP kada ta karbi Sanata Kalu da gwamnan Ebonyi.

A cewarsa waɗan nan mutanen sun gano cewa sun yi kuskuren sauya sheka zuwa APC shiyasa suke son dawo wa PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel