Da Dumi-Dumi: Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

Da Dumi-Dumi: Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, yace gwamna Ganduje ya ci amanarsa duba da irin halaccin da ya masa
  • Kwankwaso ya bayyana cewa rikicin APC a jihar Kano ya samo asali ne daga son kai na Ganduje
  • Jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya kuma nuna jin daɗinsa bisa kalaman da Sanata Shekarau ya yi a kansa

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace rikicin da ya baibaye jam'iyyar APC reshen Kano bai zo masa da mamaki ba.

Vanguard tace Kwankwaso ya ɗora laifin akan gwamnan Kano na yanzu, Dakta Abdullahi Ganduje, inda yace halinsa na son kai ya jawo wannan rikicin.

Tsohon sanatan Kano ta tsakiya ya bayyana cewa dama yasan lokaci ne kawai amma za'a zo dai-dai nan a jam'iyyar APC sabida abubuwa da dama da ake yi a cikinta.

Kara karanta wannan

Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

Ganduje da Kwankwaso
Da Dumi-Dumi: Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwankwaso yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk wanda ya gaza rungumar wanda ya masa halacci tsawon shekaru, domin shi kansa yasan mun masa halacci, amma da ya samu dama lokaci ɗaya, sai ya kasa jure rike Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya."

Sanata Kwankwaso yace rikicin dake faruwa cikin jam'iyyar APC mai mulki ya samo asali ne daga tsantsar son rai.

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya kira yanayin da APC ta tsinci kanta da karin magana a Hausa, "Karya fure take ba ta ƴaƴa."

Na ji daɗin kalaman Shekarau - Kwankwaso

A wata zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya bayyana cewa ya ji daɗin kalamai masu kyau da tsohon gwamna, Sanata Ibrahim Shekarau, ya yi a kansa.

"An faɗa mun kalaman da ya yi a kaina, amma ina cikin godiyar Allah. Kalamansa sun nuna kamar komai bai faru ba a baya, yanzun Allah ya haskaka masa."

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP

"Duk mutum mai hankali da akaiwa irin haka zai ji farin ciki. Bacin haka nasan kalaman da ya faɗa dagaske yake kuma har zuciyarsa."
"Idan siyasa ta sake haɗa mu watarana, zamu cigaba da tafiya tare, idan kuma hakan ba ta samu ba, zamu gode wa Allah tun da an samu cigaba."

Yadda Ganduje ya ci amana ta - Kwankwaso

Da yake amsa tambayar cewa ko yaga sakon taya murnar Ganduje lokacin da ya cika shekara 65? Kwankwaso yace bai gani ba domin aiki ya masa yawa a lokacin.

"Aiki yamun yawa ranan, ban sani ba ko dama haka halinsa yake tun farko, amma da abun bai kai matakin nan ba. Ba wanda zai tsammanin akwai ranar da Ganduje zai banɗare mun."
"Ina da kyakkyawar alaƙa da kowa har da Ganduje, haka na bar gwamnatin Kano na tafi ma'aikatar tsaro. Lokacin ya tafi Chadi, amma na kira shi, nace ya dawo mu yi aiki tare."

Kara karanta wannan

An damke Lauyan bogi bayan shekaru 10 yana zuwa kotu aiki

"Da ya dawo na bashi Fom ɗin mataimakin gwamna, na yi haka saboda shine dattijo ba tare da ya bani ko sisin kwabo ba domin a Kwankwasiyya bama karɓan kudin kowa."

Kwankwaso ya ciji yatsa cewa duk da halaccin da ya yi wa Ganduje, amma yanzun sam ba su ga maciji da juna.

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta yi karin haske kan dalilin da yasa ta nemi da damke hadimin Sanata Ɗanjuma Goje

Kakakin APC reshen jihar Gombe, Moses Kyari, yace jam'iyya ta ɗauki mataki kan Yayari ne saboda yaɗa ƙanzon kurege a soshiyal midiya.

Haka nan yace babu hannun gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe a zancen kama hadimin tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel