Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

  • Wani Fasto ya hada baki da bata gari wajen garkuwa da babban fasto da amsan kudin fansa
  • Matashin faston wanda yayi nadamar abinda yayi ya bayyana cewa bai taba tunanin za'a kama shi ba
  • Ya nemi gafarar al'umma bayan furta cewa yanzu ya zama abin kunya ga addinin Kirista da iyalinsa

Owerri - Jami'an hukumar yan sanda sun cika hannu da wani matashin Fasto Izuchukwu Anoloba kan zargin garkuwa da babban Fada na Katolika, Fr Fidelis Ekemgba a jihar Imo.

Matashin Faston mai shekaru 35 ya amsa laifin da yayi inda yace ya samu nashi rabon na N1.5m kudin fansan da aka biya.

Kwamishanan yan sandan jihar, Rabiu Hussaini, ya bayyana Faston gaban manema labarai, rahoton DailyTrust.

A cewarsa, sai da aka biya kudin fansa N5m aka saki Bishop din.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

Ya kara da cewa Bishop din ya kasance Shugaban Cocin St. Peters Catholic Parish a garin Umunohu Amakaohia dake karamar hukumar Ihitte/Uboma ta jihar.

Matashin Fasto ya yi garkuwa babban Bishop na Katolika a jihar Imo
Matashin Fasto ya yi garkuwa babban Bishop na Katolika a jihar Imo
Asali: Facebook

Faston da ya aikata laifin ya bukaci a yafe masa bisa wannan abin kunya da yayi.

Yace:

"Ni Fasto ne a Cocin Apostolic dake Legas. Na samu N1.5m daga garkuwa da Bishop. Ban taba tunanin za'a kama ni ba. Na yi nadamar abinda nayi saboda na zama abin kunya ga Kiristoci da iyali na."

Birtanita ta fitar da sabbin shawarin tafiye-tafiye, ta ja kunne kan jihohi 12 na Najeriya

Gwamnatin Ingila ta shawarci 'yan kasar ta kan ziyara ko tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin Najeriya saboda matsalar tsaro.

A wani shawarin tafiye-tafiye da suka saki a ranar Alhamsi, 2 ga watan Disamba, ofishin Foreign, Commonwealth & Development, FCDO, ya shawarci 'yan kasan a kan ziyara zuwa jihohi 12.

Jihohin sun hada da Gombe, Adamawa, Yobe, Borno, Kaduna, Katsina, Zamfara, Delta, Bayela, Akwa Ibom, Rivers da Cross Rivers.

Asali: Legit.ng

Online view pixel