An damke Lauyan bogi bayan shekaru 10 yana zuwa kotu aiki

An damke Lauyan bogi bayan shekaru 10 yana zuwa kotu aiki

  • Dubun wani mutumi a Fatakwal, birnin jihar Rivers ya cika bayan kwashe shekaru koma yana aikin lauya
  • An kama mutumin mai suna Stanley Ejirogene ne yayin amsa tambayoyi cikin kotu amma ya gaza fadan sunar jami'ar da yayi karatu
  • Stanley ya kwashe shekaru goma yana shiga kotu yin aiki amma ya gaza fadan makarantar da ya samu horo

Rivers - Wani mutum mai ikirarin shi lauya ne ya shiga hannu a Fatakwal cikin harabar kotu ranar Laraba, 1 ga Disamba, 2021.

Abokan aikin Stanley Ejirogene lauyoyi ne suka damkeshi lokacin da ya kasa ambatan jami'ar da yayi karatu da kuma makarantan lauyan da ya halarta.

Instablog9ja ta saki bidiyon mutumin a shafin Instagram inda aka yi bayanin abinda ya faru.

Lauyan bogi bayan shekaru 10 yana zuwa kotu aiki
An damke Lauyan bogi bayan shekaru 10 yana zuwa kotu aiki Hoto: Instablog9ja
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar lauyoyin Fatakwal, Prince Nyekwere, ya ce asirin mutumin ya sake tonuwa ne lokacin da aka nemi sunansa aka rasa kan shafin yanar gizon Kotun Koli da NBA.

Shugaban kungiyar lauyoyin ya bukaci Alkali C. Nwogu ya garkame mutumin cikin kurkuku har zuwa lokacin da za'a kammala bincike.

A bidiyon, mutumin yace shi fa karya ake masa, shi kwararren lauya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel