Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP

Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP

  • Jigon jam'iyyar hamayya PDP a jihar Abia, Dakta Nkole, ya gargaɗi PDP kada ta karbi Sanata Kalu da gwamnan Ebonyi
  • A cewarsa waɗan nan mutanen sun gano cewa sun yi kuskuren sauya sheka zuwa APC shiyasa suke son dawo wa PDP
  • Yace baki ɗayansu kaya ne kuma ba su da tabbas a siyasance, dan haka idan suka shigo zasu tarwatsa PDP

Abia - Jigon jam'iyyar PDP a jihar Abia, Dakta Isaac Nkole, ya gargadi jam'iyyarsa kada ta sake amincewa da Sanata Orji Uzor Kalu, ya dawo cikin PDP.

Vanguard ta rahoto cewa Nkole ya yi wannan gargaɗin ne yayin zantawa da manema labarai a Umahia, babban birnin Abia.

Yace tsohon gwamnan ya ƙagu ya sake dawo wa PDP bayan gano cewa tashi ta ƙare a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kwankwaso ya yi magana kan rikicin Ganduje da Shekarau a APC jihar Kano

Jam'iyyar PDP
Jigon PDP ya bayyana sunayen gwamnan APC da tsohon gwamna dake shirin sauya sheka zuwa PDP Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Nkole ya kara da cewa sanatan ya jima yana bibiyan masu ruwa da tsaki a matakin jiha da kuma ƙasa, yana rokon su bashi dama ya koma PDP

This Day ta rahoto a jawabinsa yace:

"Ina baiwa shugabancin PDP a jihar Abia da kasa shawara, kada su kuskura su bar sanata Orji Uzor Kalu ya dawo cikin PDP, domin shigowarsa zai tarwatsa jam'iyyar."
"Ina faɗin haka ne saboda naji labarin ya fara bibiyar jiga-jigan PDP a kowane mataki, yana rokon su ba shi damar sake koma wa cikin jam'iyyar."
"Yasan cewa lokacinsa ya kare a APC, saboda tsaginsa ba shine uwar jam'iyya a Abuja ta amince da shi ba. Sanin abubuwan da yasa a gaba a 2023, shiyasa ya matsu ya dawo PDP amma mu bamu bukatar shi."

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa muka nemi yan sanda sun cafke hadimin Danjuma Goje, Jam'iyyar APC ta magantu

Wane gwamna ne kesom komawa PDP?

A cewar Nkole, Sanata Kalu ba shi kaɗai bane jigon APC daga yankin Kudu maso Gabas dake kokarin komawa PDP.

Ya yi ikirarin cewa gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya fara tuntubar masu ruwa da tsaki a kokarinsa na ficewa daga APC ya dawo PDP.

"Mun samu labarin gwamna Dave Umahi na son dawo wa PDP. Gaba ɗayansu sun gane gaskiya yanzun, sun gane kuskurensu na sauya sheka zuwa APC."
"Wannan ne yasa suke kokarin sake dawo wa PDP, amma PDP ta gaji da irinsu marasa tabbas a tafiyarta."

A wani labarin kuma Yan sanda sun damke mutum 13 da hannu a ƙone ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau

Hukumar yan sanda reshen Kano ta tabbatar da cewa ta shawo kan halin da aka shiga bayan harin yan daba a Ofishin APC.

Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace jami'an da hukumar ta tura sun cafke mutum 13 tare da kwato wasu makamai.

Kara karanta wannan

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel