Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

  • Wata kotun majistare a jihar Gombe ta tasa keyar wani hadimin Goje zuwa gidan yari bisa laifin yada karya
  • An tuhumi Muhammad Adamu Yayari da laifin yada rubutun da bai dace ba a asusunsa na kafar Facebook
  • An tura shi gidan yari bayan sauraran kara, inda aka dage ci gaba da batun har sai ranar 6 ga watan Disamba

Gombe - A ranar Talatar da ta gabata ce wata kotun majistare ta tasa keyar wani hadimin Sanata Muhammad Danjuma Goje, Muhammad Adamu Yayari a gidan yari bisa laifin sanya takardun murabus din wasu shugabannin jam’iyyar APC daga Yamaltu/Deba a shafinsa na Facebook.

An kama Yayari, wanda shi ne hadimi na musamman ga Sanatan kan sabbin kafafen yada labarai, tare da tsare shi a hedikwatar ‘yan sandan jihar Gombe a ranar Litinin din da ta gabata, biyo bayan karar da sakataren jam’iyyar APC na jihar, Abubakar Umar S Goro ya kai.

Kara karanta wannan

Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin

Taswirar jihar Gombe
Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda (FIR), wanda ake zargin a ranar 25 ga Nuwamba, 2021 ya wallafa kalaman karya a kan shugabannin jam’iyyar APC a karamar hukumar Yamaltu/Deba a shafin sa na Facebook, Daily Trust ta ruwaito.

Lauyan jihar, Ramatu Ibrahim Hassan, wacce ta karanto bayanan hukumar ‘yan sanda ta FIR, ta ce wanda ake tuhumar ya yi niyyar bata sunan shugabannin unguwanni da rubutun nasa, inda ya yi zargin cewa 80% cikin 100% sun “yi murabus” daga mukaminsu.

Ta shaida wa kotun cewa Yayari ya aikata laifukan yada karya da tada hankali wanda ya saba wa sashe na 393 da 114 na dokar Penal Code.

Lokacin da kotu ta tambaye shi ko bayanin da ake tuhumarsa akai na cikin FIR gaskiya ne, wanda ake zargin ya ki amsa laifinsa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Bayan haka, lauyoyin da ke kare shi, Barista Sa’idu Mu’azu Kumo da A. B. El-Ibrani suka nemi belin sa.

Sai dai Ramatu Hassan ta ki amincewa da neman belin inda ta shaida wa kotun cewa zai zama illa idan aka saki wanda ake tuhuma bisa la’akari da yanayin shari’ar.

Alkalin kotun, Cif Majistare Mohammed Sulaiman Kumo, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 6 ga watan Disamba domin duba bukatar ba da belinsa, sannan ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsare Yayari ya biyo bayan wani sakon da ya wallafa a Facebook ranar Alhamis, lokacin da wasu shugabannin jam’iyyar APC daga karamar hukumar Yamaltu/Deba suka yi murabus daga mukamansu.

Da Legit.ng Hausa ta yi duba zuwa ga asusun Facebook na hadimin na Goje, ta ga inda Yayari ya rubuta sanarwar da ke bayyana 80% na shugabannin APC a Yamaltu/Deba sun yi murabus.

Kara karanta wannan

FG ta zargi ESN da yanka wasu ‘yan sanda tare da yada bidiyon gawarwakinsu a intanet

Kashi 80% na shugabannin APC a Gombe sun yi murabus kan rikicin Goje da Inuwa

A baya, rahotanni daga Gombe na nuna cewa sama da 80% cikin 100 na shuwagabannin APC daga karamar hukumar Yamaltu/Deba sun yi murabus daga mukamansu sakamakon takaddamar Sanata Danjuma Goje da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a kwanakin baya.

Shugabannin sun sanar da matakin ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba bayan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron, tsohon shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, Alhaji Sulaiman Ibrahim, ya ce shugabannin unguwannin sun yi murabus daga ofisoshinsu ne saboda rashin mutunta Goje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel