Yanzu-Yanzu: Kashi 80% na shugabannin APC a Gombe sun yi murabus kan rikicin Goje da Inuwa

Yanzu-Yanzu: Kashi 80% na shugabannin APC a Gombe sun yi murabus kan rikicin Goje da Inuwa

  • Rikicin siyasa tsakanin Sanata Danjuma Goje da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi sanadiyar jikkatar jam'iyya
  • Shugabannin jam’iyyar APC 'yan tsagin Sanatan sun mika takardar murabus dinsu a karamar hukumar Yamaltu/Deba da ke jihar
  • Shugabannin jam’iyyar sun ce ba za su iya ci gaba da kallon ana cin mutuncin shugaban nasu a jihar Gombe ba

Gombe – Rahotanni daga Gombe na nuna cewa sama da 80% cikin 100 na shuwagabannin APC daga karamar hukumar Yamaltu/Deba sun yi murabus daga mukamansu sakamakon takaddamar Sanata Danjuma Goje da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a kwanakin baya.

Shugabannin sun sanar da matakin ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba bayan taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Sanata Goje da Gwamna Inuwa
Yanzu-Yanzu: Kashi 80 na 'yan APC a Gombe sun bar jam'iyyar saboda rikicin Goje da Inuwa | Hoto: Gombe state government
Asali: Twitter

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron, tsohon shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, Alhaji Sulaiman Ibrahim, ya ce shugabannin unguwannin sun yi murabus daga ofisoshinsu ne saboda rashin mutunta Goje.

Kara karanta wannan

Buni ya bayyana dalilai 5 da suka sanya Buhari kai babban taron APC watan Fabrairun 2022

Hakazalika, ya ce kai wa ayarin motocin Sanata Goje hari, makonni uku da suka gabata na daga cikin dalilin yin murabus dinsu.

Ya ce shugabannin jam’iyyar APC sun cimma matsayar ne bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga karamar hukumar.

Shugabannin sun yi Allah-wadai da harin da aka kai wa Goje, inda suka ce suna bayan Sanatan bisa la’akari da irin rawar da ya taka wajen ci gaban jihar Gombe da kasa baki daya.

Ya kara da cewa, ga ’ya’yan jam’iyyar da ke jihar, Sanata Goje shi ne daya tilo shugaban jam'iyyar da aka amince da shi, kuma ya cancanci a girmama shi sosai idan aka yi la’akari da irin rawar da ya taka wajen kafa jam’iyyar da kuma raya ta.

Yace:

“A gaskiya ma, babbar rawar da ya taka ne ta kai ga fitowar Muhammad Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar da kuma nasarar da jam’iyyar ta samu a dukkan matakai.

Kara karanta wannan

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

“Saboda haka, a matsayinmu na shugabannin siyasa na APC a unguwanni 11 na karamar hukumar Yamaltu/Deba. Don haka muna tabbatar da goyon bayanmu da biyayyarmu ga Sanata Goje a matsayin fitaccen shugaban jam’iyyar APC a jihar Gombe na gaskiya.”

Goje ya tafi kotu, ya roki Malami ya bi masa kadunsa bisa neman hallaka shi da aka yi

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltan Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje ya nemi Sufeto Janar na 'yan sanda, Alkali Baba da babban Atoni Janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami da su binciki harin da aka kai masa.

Goje ya yi zargin cewa harin da aka kai masa a Gombe yunkuri ne na hallaka shi da hadiminsa, Adamu Manga.

Ya yi zargin cewa dogarin gwamna Inuwa Yahaya, Zulaidaini Abba da shugaban tsaron gwamnan, Sani Bajoga sune manyan wadanda ake zargi, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel