Bukola Saraki ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na takarar shugaban kasa a 2023

Bukola Saraki ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na takarar shugaban kasa a 2023

  • Jiga-jigan jam'iyyar PDP na yankin arewa ta tsakiya sun nuna goyon bayan su ga takarar Bukola Saraki a zaɓen 2023
  • Shugaban tawagar masu ruwa da tsaki na PDP, Farfesa Hagher, yace Saraki matashi ne mai kwarewa irin wacce ake bukata
  • Shugaban PDP na yankin, Theophilus Dakarshan, yace lokaci ya yi da ɗan yankin su zai shugabanci Najeriya

Lafia, Nasarawa - Masu ruwa da tsaki na jam'iyyar hamayya PDP daga yankin arewa ta tsakiya sun bayyana tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukula Saraki a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a 2023.

Da yake jawabi ranar Litinin a Lafiya, shugaban tawagar masu ruwa da tsaki, Farfesa Iyorwuese Hagher, yace a halin yanzun suna bukatar Saraki, kamar yadda Punch ta rahoto.

Bukola Saraki
Bukola Saraki ya samu gagarumin goyon baya a shirinsa na takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya kara da cewa Saraki ne ya dace ba wai wanda yake tafiya kasashen duniya a lokuta da dama yana ɓannatar da dukiyar ƙasa wajen neman lafiya ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

This Day ta ruwaito yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bukola Saraki matashi ne mai tasowa kuma yana da ɗumbin kwarewa a kowane mataki na gwamnati da zai iya gyara Najeriya."
"Ba mu bukatar tsohon mutum a matsayin shugaban ƙasa, wanda zai dinga fita kasa a koda yaushe domin duba lafiyarsa kuma yana ɓannatar da dukiyar kasa."

Shin Saraki zai iya jagorancin Najeriya?

Daga nan kuma ya yi kira ga sauran sassan ƙasar nan, waɗan da a baya arewa ta tsakiya ta mara musu baya, su yi duk me yuwu wa wajen tallafawa takarar Saraki a 2023.

Farfesa Hagher yace Bukola Saraki yana da duk wata kwarewa da cancantar da ake bukata ya shugabanci ƙasar nan a 2023.

Yankin mu ya kamata a kai shugaban kasa

A nasa jawabin, shugaban jam'iyyar PDP na yankin arewa ta tsakiya, Theophilus Dakarshan, yace an bar yankinsu a baya wajen samar da shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

Saboda haka ne ya yi kira ga yan Najeriya su goyi bayan wani daga yankin ya zama shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta dare gida biyu, Matasa sun tsige Mala Buni sun nada sabon shugaba

Rikicin jam'iyyar APC ta ƙasa ya bude sabon shafi, yayin da matasan jam'iyyar suka sanar da rushe kwamitin rikon kwarya na Mala Buni.

Matasan karkashin kungiyarsu PYM, sun kuma rantsar da sabbin shugabanni da mambobin sabon kwamitin rikon kwarya da suka naɗa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel