Babbar Magana: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu, Matasa sun tsige Mala Buni sun nada sabon shugaba

Babbar Magana: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu, Matasa sun tsige Mala Buni sun nada sabon shugaba

  • Rikicin jam'iyyar APC ta ƙasa ya bude sabon shafi, yayin da matasan jam'iyyar suka sanar da rushe kwamitin rikon kwarya na Mala Buni
  • Matasan karkashin kungiyarsu PYM, sun kuma rantsar da sabbin shugabanni da mambobin sabon kwamitin rikon kwarya da suka naɗa
  • Mataimakin kakakin APC na ƙasa, Yekini Nabena, yace kungiyar matasan ba ta da ikon rushe kwamitin Buni

Abuja - Rikicin jam'iyyar APC mai mulki ya bude wani sabon babi ranar Litinin yayin da matasa suka sanar da rushe kwamitin rikon kwarya na Gwamna Buni.

Matasan karkashin kungiyar Progressive Youth Movement (PYM), sun tsaida ranar 26 ga watan Fabrairu a matsayin ranar gangamin taron APC na ƙasa.

Dailytrust ta rahoto cewa kungiyar matasan APC ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ta kira a Abuja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Dan majalisar dokoki na jam'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Mala Buni
Ana wata ga wata: Jam'iyyar APC ta dare gida biyu, An sauke Mala Buni daga mukaminsa an naɗa wani Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Wa suka naɗa sabon shugaban APC na riko?

Da yake jawabi, sabon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Prince Mustapha Audu, wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan Kogi, Abubakar Audu, ya bayyana cewa sun fito ne domin ceto APC daga rushewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Yau mun zo rantsar da kwamitin rikon kwarya PYM–CECPC, waɗan nan matasa maza da mata da muka zaba mun ɗora musu alhakin yin duk me yuwu wa wajen ganin mun gudanar da gangami kafin karshen watan Fabrairu, 2022."

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da, mataimakin shugaba (arewa), Tukur Tukur Buratai, mataimakin shugaba (kudu), Busayo Akinnadeju.

Kazalika matasan sun kuma naɗa wakilai daga kowane yankin kasar nan, daga cikinsu har da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran su.

Kwamitin APC ya maida martani

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ranar Litinin zamu dawo da Sabis jihar Zamfara, Matawalle

Da yake martani kan lamarin, mataimakin kakakin APC na ƙasa, Yekini Nabena, yace matasa ba su da karfin ikon rushe kwamitin da Buni ke jagoranta.

Ya kuma ƙara da cewa kungiyar matasan ba ta daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC (NEC), kamar yadda Vanguard ta rahoto.

An rantsar da kwamitin Buni a watan Juni 2020 bayan rushe shugabancin Adams Oshiomhole, da zummar kwamitin zai shirya babban gangamin jam'iyya.

Amma sama da shekara ɗaya kenan, har yanzun kwamitin ya gaza shirya babban taron, wanda za'a zaɓi sabbin shugabanni na ƙasa.

A wani labarin kuma gwamnan Kaduna ya roki yan Najeriya kada su kuskura su zaɓi jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023 dake tafe

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya gargaɗi yan Najeriya musamman mutanen Kaduna kada su zabi PDP a 2023.

El-Rufa'i ya roki al'ummar jihar Kaduna su yarda da shi, zai zabar musu wanda ya dace ya gaji kujerarsa a 2023.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda

Asali: Legit.ng

Online view pixel