2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci jihar Benue a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba
  • Saraki ya je Benue ne domin tuntuba tare da sanar da aniyarsa na son takarar kujerar shugaban kasa a 2023
  • Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya samu rakiyar manyan jiga-jigan PDP a tafiyar

Jihar Benue - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, kan kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Saraki wanda yayi ganawar sirri da Ortom ya kuma gana da kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP a jihar domin sanar da su kudirinsa na fara tuntuba game da aniyarsa na shugabantar kasar, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Wa'adin shigar da kara ya kusa karewa, APC ba ta shigar da kara ba

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari
2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya bayyana cewa sauya shekar da masu biyayya ya jam’iyyar All Progessives Congress (APC) ke yi zuwa PDP a fadin kasar alamu ne da ke nuna cewa jam’iyyar na iya zama babu kowa kafin zabe mai zuwa.

Saraki ya ce:

“Jam’iyyar da ta gaza tsara harkokinta bata da hurumin jagorantar wannan kasa. Jam’iyyar da ta tsara harkokinta ya shirya jagorantar wannan kasa kuma ita ce PDP.”

Ya kara da cewa yankin arewa ta tsakiya ta sauke hakkinta ta hanyar aiki tukuru don ganin dorewar hadin kan kasar a matsayin tsintsiya madaurinki daya inda yace:

“A wannan karon, ya zama dole mu tsaya a bayan namu kuma daga gida ake fara tarbiya.”

Tsohon gwamnan na jihar Kwara, wanda ya samu rakiyar jiga-jigan PDP ya yi godiya ga gwamnan na Benue a kan tsayawa yankin.

Kara karanta wannan

APC ta ba Buhari wuka da nama na tsayar da lokacin gudanar taron gangami

Cikin wadanda suka yi masa rakiya akwai tsohon gwamnan jihar Kogi, Idris Wada, tsohon shugaban PDP na kasa, Kawu Baraje, Sanata Suleiman Adokwe da Farfesa Iyorwuese Hagher, shugaban kwamitin kamfen din Saraki na takarar shugaban kasa.

A ruwayar Vanguard, Ortom ya jinjinawa Saraki kan kasancewa daya daga cikin yan Najeriya da suka mayar da gudunmawa wajen ci gaban damokradiyya.

Gwamnan ya ce lokaci ya yi da za a ceto kasar daga kasa, wajen gwamnatin APC ta kai ta zuwa sama, inda ya kara d cewa Saraki ya cancanci ceto kasar daga halin da take ciki a yanzu.

A nasa bangaren, shugaban PDP a jihar, Sir John Ngbede, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Isaac Mfo, ya ce jam’iyyar na nan yadda take yayin da ya ba mai neman takarar shugaban kasar tabbacin marawa aniyarsa na shugabantar kasar baya.

Najeriya ba za ta iya juran azabtarwar APC na karin shekaru hudu ba, inji PDP

Kara karanta wannan

Sanata Walid Jibril: Za mu fatattaki jam'iyyar APC a 2023

A wani labarin, gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun ce Najeriya ba za ta iya jure wasu shekaru hudu a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba, rahoton Daily Trust.

Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana hakan a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba a wajen bude wani taron jam’iyyar na kwana biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel