Da Duminsa: 'Yan majalisar dokokin Filato za su yi zaman sulhu yau Alhamis

Da Duminsa: 'Yan majalisar dokokin Filato za su yi zaman sulhu yau Alhamis

  • Majalisar dokokin jihar Filato za ta zauna zaman sasanta tsakanin 'yan majalisun da suke rikici bayan tsige kakakin majalisar
  • Ana ta rikici a majalisar dokokin jihar Filato tun a watan Oktoba bayan da majalisar ta tsige shugabanta
  • Ana sa ran yau Alhamis 25 ga watan Nuwamba majalisar dokokin za ta kawo karshen sabanin da ke tsakanin junansu

Filato - Alamu masu karfi sun bayyana rikicin da ya dabaibaye Majalisar Dokokin Filato ya zo karshe yayin da ake sa ran dukkan ‘yan majalisar 24 za su hallara a zaman majalisar na ranar Alhamis, inji rahoton ThisDay.

Majiyoyin da ke kusa da tsigaggen shugaban majalisar Abok Ayuba sun ce watakila kungiyar tsoffin shugabannin majalisar ta yi sulhu tsakanin ‘yan majalisar da ke takun saka da shugabannin majalisar tun a watan Oktoba.

Read also

'Yan majalisa sun nuna damuwa, sun bukaci sojoji da 'yan sanda su dakile hare-hare a hanyar Kaduna-Abuja

Taswirar jihar Filato
Da Duminsa: 'Yan majalisar dokokin Filato za su yi zaman sulhu yau Alhamis | Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

Dan tsagin Abok, Hon. Sohchang Zingtim, ya tabbatar wa jaridar The Nation cewa yarjejeniyar zaman lafiya ta tabbata.

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Akwai wani abu kamar haka. Muna hanyar komawa Jos amma ba zan iya gaya muku lokacin da za a fara zama ba, amma akwai wani abu makamancin haka."

Shugaban masu rinjaye, wanda dan tsagin kakakin majalisar ne Sanda, Hon. Naanlong Daniel, shi ma ya tabbatar da cewa 'yan majalisa 24 za su kasance a zaman majalisar.

Sai dai kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP guda 9 na halartar wani taro na kasa a Abuja.

Daniel yace:

"Don haka, mai yiwuwa, ya kamata mu iya zama mako mai zuwa, idan ba zai yiwu ba a yau.
"Yayin da nake magana, ina kan hanyata ta zuwa Majalisa don shiga cikin sauran membobin."

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

Read also

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

A wani labarin, rikicin da aka yi a majalisar dokokin Filato ya dauki wani yanayi mai ban tsoro a ranar Litinin yayin da jami’an tsaro suka kame tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar, Abok Ayuba da wasu ‘yan majalisa 10 da ke masa biyayya.

Da misalin karfe 3:15 na rana, kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, ya tasa ‘yan tawagar tsohon kakakin majalisar su 11 a motocin Hilux guda hudu, The Nation ta ruwaito.

Idan baku manta ba, a ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu 'yan majalisu a jihar suka tsige shugaban majalisar, lamarin ya jawo cece-kuce da gardama, Daily Trust ta ruwaito.

Source: Legit

Online view pixel