Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

Bayan tsige shi, 'yan sanda sun kame shugaban majalisar dokokin Filato da tawagarsa

  • 'Yan sanda sun kame tsigaggen shugaban majalisar dokokin jihar Filato bayan ballewar rikici
  • An kame shi tare da wasu mambobin majalisar su 10 a tare dashi, inda aka tafi dasu wani wuri
  • Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a san inda 'yan sanda suka wuce da 'yan majalisar ba

Jos, Filato - Rikicin da aka yi a majalisar dokokin Filato ya dauki wani yanayi mai ban tsoro a ranar Litinin yayin da jami’an tsaro suka kame tsigaggen kakakin majalisar dokokin jihar, Abok Ayuba da wasu ‘yan majalisa 10 da ke masa biyayya.

Da misalin karfe 3:15 na rana, kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, ya tasa ‘yan tawagar tsohon kakakin majalisar su 11 a motocin Hilux guda hudu, The Nation ta ruwaito.

Idan baku manta ba, a ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu 'yan majalisu a jihar suka tsige shugaban majalisar, lamarin ya jawo cece-kuce da gardama, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Zanga-Zangar Matasa a majalisar dokoki ta dauki sabon salo, An fara harbe-harbe

Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun kame tsigaggen shugaban majalisar dokokin jihar Plateau
Yanzu-Yanzu: 'Yan sanda sun kame tsigaggen shugaban majalisar dokokin jihar Plateau
Asali: UGC

‘Yan majalisar, sun ce:

“Muna tsaye, tsayin daka kan ayyukanmu ga al’ummar Filato da suka zabe mu a majalisa a fafutukar da muke yi na ganin an cimma matsaya mai ma’ana har sai an dawo da Shugaban Majalisar.”

Memba mai wakiltar Langtang ta Kudu, Hon Zingtin Sohchang ya ce:

"Yanzu jami'an tsaro suka hada mu a cikin motocin Hilux hudu zuwa inda bamu sani ba, kuma idan bayan mintuna 20 kuka kira mu bamu amsa ba, to ku sani cewa an kai mu wurin da ba a sani ba."

Abok, da manema labarai suka dame shi da tambayar ko an kama shi, ya amsa da cewa:

“Ba zan iya cewa ba a halin da nake ciki yanzu ba.”

Jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan ne suka yi gaba da shi da ‘yan majalisa 10 daga harabar majalisar ta kofar baya ta kudu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya dira birnin Glasgow, Kasar Birtaniyya da asubancin Litinin

A yayin hada wannan rahoton, jami'an tsaro sun watsawa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a harabar majalisar.

Bani da hannu a tsige Kakakin Majalisa, Lalong ya maida martani

A baya kadan, Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya musanta duk wani zargi da ake cewa yana da hannu a lamarin tsige tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Filato raanr Alhamis da ta gabata.

Lalong ya yi wanna furuci ne domin kore duk wata jita-jita da take yawo a kafafen sada zumunta cewa shine ya sa aka tsige kakakin majalisan.

Wannan na kunshe ne a wani rubutu na karin haske da gwamnatin Fitato ta fitar a shafinta na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel