Jam'iyyar APGA ta yi magana kan shirin sauya shekar Gwamnan Anambra, Obiano da Saludo zuwa APC

Jam'iyyar APGA ta yi magana kan shirin sauya shekar Gwamnan Anambra, Obiano da Saludo zuwa APC

  • Jam'iyyar APGA ta yi karin haske kan raɗe-radin da ake yaɗawa cewa gwamna Obiano da Soludo zasu koma APC
  • Tun bayan kammala zaben gwamnan Anambra, jita-jita ta fara yawo cewa dama can sun sasanta da Buhari cewa zasu koma APC
  • APGA ta kira wannan jita-jita da karya tsagwaronta da wasu suka kirkira kuma suka jingina wa mutanen biyu

Anambra - Jam'iyyar APGA ta musanta raɗe-raɗin shirin sauya sheka na gwamnan Anambra mai ci, Willie Obiano, da zaɓaɓɓen gwamna, Chukwuma Soludo, zuwa APC mai mulki.

Shugaban gudanarwa na APGA ta ƙasa, Chinedu Obigwe, shine ya musanta labarin a wani taron manema labarai da ya gudana a Awka, jihar Anambra.

Punch ta rahoto jigon APGA ya bayyana jita-jitar da ake yaɗawan da wata kirkirarran ƙarya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalilin da yasa wajibi shugaba Buhari da Arewa su goyi bayan Bola Tinubu a 2023

Obiano da Soludo
Jam'iyyar APGA ta yi magana kan shirin sauya shekar Gwamnan Anambra, Obiano da Saludo zuwa APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwanaki kaɗan bayan kammala zaben Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba, mutane suka fara yaɗa cewa Gwamna Obiano da Soludo zasu koma APC.

A cewar masu yaɗa labarin, wannan na cikin sharuɗɗan yarjejeniyar da suka yi da shugaban kasa na gudanar da sahihin zaɓe.

Shin dagaske an yi wannan yarjejeniya?

Tribune Online ta rahoto Obigwe yace:

"Yana da kyau mu faɗa muku cewa yakin da Gwamna Obiano ya yi a ranar 6 ga Nuwamba yaƙi ne na ceto APGA da kuma tabbatar da kasancewarta jam'iyyar Igbo guda ɗaya tilo."
"Babu lokacin da gwamna Obiano ya yi wa wani alƙawarin matukar Soludo ya lashe zaɓe, to gaba ɗayansu zasu koma jam'iyyar APC."
"Gwamna Obiano yana da kyakkyawar alaƙa da gwamnatin shugaba Buhari, domin amfanin jiharsa ta Anambra. Buhari yasan gaskiya cewa Obiano ne jagoran APGA."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro sama da 100 a jihar Benuwai

Shin Buhari ya nemi gwamnan ya koma APC?

Obigwe ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Buhari bai taɓa neman Gwamna Obiano ya koma APC ba saboda yasan ba zai kyale APGA ya koma wata jam'iyya ba.

"Abu ɗaya Obiano ya yi don cigaban APGA a zaben da ya gudana shine samun goyon bayan shugaba Buhari wajen tabbatar sahihin zaɓe."
"Farfagandar rashin waye wa ne wani ya fito yace Gwamna Obiano zai koma APC tare da Soludo."

A wani labarin kuma Gwamna ya caccaki Buhari da gwamnatinsa, yace basu kaunar kawo karshen matsalar tsaro

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed na jihar Bauchi, yace gwamnatin Najeriya zata iya kawo karshen matsalar tsaro idan ta so.

A cewarsa matukar gwamnati zata iya datse dukkan hanyoyin sadarwa a wurraren da lamarin ya yi kamari, to komai mai sauki ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel