Gaskiya ta fito: Dalilin da yasa wajibi shugaba Buhari da Arewa su goyi bayan Bola Tinubu a 2023

Gaskiya ta fito: Dalilin da yasa wajibi shugaba Buhari da Arewa su goyi bayan Bola Tinubu a 2023

  • Ba abin mamaki bane yadda masu ruwa da tsaki da kuma jiga-jigan APC suke cigaba da nuna goyon bayan su ga Tinubu
  • Wata kungiyar matasan APC ta bayyana cewa shugaba Buhari da Arewa kansu ba zasu iya juya wa Tinubu baya ba saboda wani dalili
  • A cewar kungiyar Bola Tinubu ya yi wa APC bauta wadda ya cancanci samun goyon baya har ya samu nasara a 2023

Abuja - Ga dukkan alamu komai na tafiya kamar yadda aka tsara shi kuma ake tsammani game da takarar Asiwaju Bola Tinubu gabanin babban zaben 2023.

Guardian ta gano cewa akwai ikirarin ko shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yankinsa na Arewa a ɗaure suke, wajibi su goyi bayan takarar Tinubu.

Kungiyar matasan APC (APCN4NYA), ita ce ta bayyana haka ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba 2021.

Read also

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Tinubu da Buhari
Daga karshe gaskiya ta fito: Dalilin da yasa shugaba Buhari, Arewa ba zasu iya juyawa Tinubu baya ba a 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Meyasa kungiyar ta yi wannan ikirarin?

A wata sanarwa da sakatare janar na kungiyar APCN4NYA, Oludayo Ogunjebe, ya fitar, yace gudummuwar da jagoran APC ɗin ya bayar, ta fi karfin a yi watsi da ita.

Oludayo ya kara da cewa Tinubu ba wai mamban jam'iyya bane kaɗai, shine ƙashin bayan jam'iyyar APC mai mulki.

Ya kuma yi ikirarin cewa a baki ɗaya yankin kudancin Najeriya, babu wanda ya cancanta, ya dace ya gaji Buhari kuma ya jagoranci Najeriya a 2023.

Abinda zaɓen 2023 ke nufi a APC?

Bugu da ƙari, Oludayo yace zaɓen 2023 zai zama tamkar yaba kyauta ne da tukuici ga Tinubu, domin saka masa da goyon baya kan gudummuwar da ya bayar.

Sakataren yace:

"Yan Najeriya sun san cewa in banda ni'imar da Allah ya mana da Asiwaju Tinubu, ina da tabbacin da yanzun ba jam'iyyar mu bace take mulki."

Read also

Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU

"Saboda haka a wurin mu, wannan lokaci ne da zai samu sakayya daga yan uwa daga dukkan yankunan da muke da su, mu goya masa baya ya jagoranci ƙasar nan domin cika kyakkyawan burinsa."
"A wurin mu, ba karamin babbar asara bace ninki biyu, idan aka ce Bola Tinubu bai samu damar gadar shugaba Buhari a 2023 ba."

A wani labarin kuma Jagoran APC Bola Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan mutum 50,000 a wannan jihar ta PDP

Shugabannin APC na shirin haɗa wa jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, mambobin APC 50,000 a jihar Ribas.

A cewar tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Okocha, zasu tabbatar da mara wa Tinubu baya har zuwa ya zama shugaban ƙasa.

Source: Legit.ng

Online view pixel