Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

  • Ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami, ya nesanta knsa da fastocin neman takarar shugaban kasa da ake yaɗawa na shi
  • A cewar hadimin ministan, Affan Abuya, ya bayyana cewa wasu makiyan ministan ne ke yaɗa fastocin
  • Yace ko kaɗan fastocin ba su fito daga karkashin kulawar ministan ba, kawai wasu ne ke son jan hankalin al'umma

Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya nesanta kansa da fastocin yakin neman takarar shugaban ƙasa da ake yaɗa wa.

Punch ta rahoto cewa Sheikh Pantami ɗan asalin jihar Gombe, wanda tsohon darakta janar ne na hukumar NITDA, kafin daga bisa Buhari ya naɗa shi minista.

A baya-bayan nan ministan ya sha fama da kalubele kan matsayin Farfesa da jami'ar fasaha ta tarayya dake Owerri (FUTO) ta ba shi a fannin Cyber Security.

Kara karanta wannan

Mun fara tattaunawa da Bankin Duniya domin karbo sabon Bashi, Shugaba Buhari

Farfesa Pantami
Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: Dr Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Wannan lamarin dai ya tafi da kujerar tsohon shugaban kungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar Gombe.

Shugaban CAN ɗin ya rasa kujerarsa ne biyo bayan fitar da sakon murna da Pantami da ya yi ba tare da amincewa shugabanni ba.

Wane martani Pantami ya yi kan Fastocin?

Bayan fastocin takarar shugaban kasa na Pantami sun watsu, wakilin Jaridar ya tuntubi hadimin ministan, Affan Abuya, kan sahihancin lamarin.

Sai dai Mista Abuya ya yi watsi da lamarin baki ɗaya, inda ya bayyana cewa wannan na daga cikin aikin yan adawan ministan.

Hadimin Farfesa Pantami ya kara da cewa fastocin na karya ne kuma an kirkire su ne dan wata manufa daban amma ba da sanin Pantami ba.

Yace:

"Waɗan nan fastocin ba daga minista sadarwa suka fito ba, wata manakisa ce daga makiyan sa kawai."

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

A wani labarin kuma Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, yace a halin yanzun ya daina sha'awar zama shugaban ƙasan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun bayan da ya bar ofishin gwamna a 2007, Bafarawa ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa akalla sau uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel