2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3

2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3

  • Yayin da 2023 ke kara matsowa, Attahiru Bafarawa yace ba ya sha'awar zama shugaban ƙasan Najeriya
  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma jigo a jam'iyyar hamayya PDP yace ba zai sake neman wata kujerar siyasa ba
  • Bafarawa ya yi kaca-kaca a halin gwamnoni na zarcewa majalisar dattijai bayan kammala wa'adin su

Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, yace a halin yanzun ya daina sha'awar zama shugaban ƙasan Najeriya.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun bayan da ya bar ofishin gwamna a 2007, Bafarawa ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa akalla sau uku.

Tsohon gwamnan ya taka takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar DPP a zaɓen shekarar 2007, amma ya sha ƙasa a hannun marigayi Umaru Yar'Adua na PDP.

Attahiru Bafarawa
2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3 Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Bafarawa, ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ACN ranar 21 ga watan Disamba, 2010, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mun fara tattaunawa da Bankin Duniya domin karbo sabon Bashi, Shugaba Buhari

Kazalika a shekarar 2019, Attahiru Bafarawa, ya nemi tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa karkashin Inuwar jam'iyyar PDP.

Bana sha'awar zama shugaban kasa - Bafarawa

A wata fira da jaridar Punch da aka buga ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, tsohon gwamnan Sokoto yace ba zai sake neman wani ofishin siyasa ba.

Da aka tambayeshi, ta wace hanya zai shawo kan matsalar tsaron Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa, Bafarawa yace:

"An yi rashin sa'a, ba zan zama shugaban ƙasa ba, kuma nima bana son zama shugaban Najeriya."

Ko meyasa ya aje kudirinsa na zama shugaban kasa?

Da yake jawabi kan dalilin ɗaukar wannan matakin, Jigon PDP yace:

"Wannan tambaya ce ta babu niyyar yin wani Abu, a lokacin da nake siyasa, lokacin ina da niyya, amma yanzun babu kwata-kwata."

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

"Ina tunanin na yi iyakar bakin kokarina lokacin da na samu dama, hakan da na samu ma ya wadace ni."
"Saboda haka ba zan sake neman wani mukamin siyasa ba har karshen rayuwata kuma ba zan karbi wani naɗin siyasa ba har karshen rayuwa ta. Amma zan bada shawara idan da bukatar haka."

Abun kunya ne bayan gwamna ka wuce sanata -Bafarawa

Tsohon gwamnan yace rashin godiyar Allah ne gwamnan ya nemi zarcewa sanata bayan kammala wa'adin mulkinsa.

Yace:

"Dan me zaka shafe shekaru 8 a kan kujerar gwamnan wata jiha a Najeriya, kuma kace zaka nemi takarar majalisar dattawa?"
"Bayan ka bada gudummuwa na shekara 8, me zai hana kabar wasu su tafi majalisar ƙasa? A matsayin tsohon gwamna, shugaban ƙasaa kaɗai ya kamata ka nema, duk abinda bai kai wannan ba rashin godiya ne da haɗama."

A wani labarin kuma Gwamnan Katsina ya bayyana dalilan da yasa mutanen kirki ba su son shiga harkokin siyasa a Najeriya

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina yace dabancin siyasa ke hana mutanen kirki shiga a dama da su.

Gwamnan ya kuma yi kira ga yan siyasa baki ɗaya su aje duk wani banbanci, su sa ilimi wajen tafiyar da harkokinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel