Mun fara tattaunawa da bankin duniya domin ciwo sabon bashin gida masarrafan rigakafi, Shugaba Buhari

Mun fara tattaunawa da bankin duniya domin ciwo sabon bashin gida masarrafan rigakafi, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya bayyana shirin gwamnatinsa na sake karbo bashi daga Bankin Duniya domin fara samar da rigakafi a Najeriya
  • Shugaban yace tuni tattaunawa ta yi nisa tsakanin gwamnati da Bankin kuma ba da jima wa ba za'a fara aikin
  • Buhari yace gwamnatinsa zata yi raga-raga da Annobar COVID19 musamman illar da tai wa tattalin arziki

Jos, Plateau - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara tattaunawa da bankin Duniya kan yadda zata sami rancen dala miliyan $30m.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban yace gwamnatin zata karbo waɗan nan kuɗaɗen ne domin gida ma'aikatar da zata samar da rigakafi a Najeriya.

Buhari ya kara da cewa za'a fara aikin ginama'aikatar sarrafa rigakafin da za'a gina bisa haɗin guiwar kamfanin May & Baker Nigeria Plc shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU

Osinbajo da Buhari
Mun fara tattaunawa da bankin duniya domin ciwo sabon bashin gida masarrafan rigakafi, Shugaba Buhari Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya faɗi haka ne a wurin yaye manyan jami'ai 43 a Jos, jihar Filato, ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron ya samu halartar gwamnan Filato, Simon Lalong, Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Saad Abubakar III, da sauran manyan mutane.

Shirin FG kan sabon bashin

Da yake jawabi ta bakin Osinbajo, Shugaba Buhari yace:

"Najeriya ta fara tattaunawa da Bankin Duniya, domin tara dala miliyan $30m, waɗan za'ai amfani da su wajen gina ma'aikatar sarrafa rigakafin COVID19."
"Kuma za'a fara aikin ginin gadan-gaban a watanni ukun farko na shekara mai shigo wa 2022."
"Wannan ma'aikatar zata cike mana gurbi kuma ta kawo karshen shigo da ɗanyun kayayyakin rigakafi da yi masa mazubi domin rarrabawa."

Shugaban ƙasan ya kara da bayyana cewa nan gaba za'a cigaba da sarrafa rigakafin baki ɗaya a Najeriya, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

Bugu da kari yace gwamnatinsa zata kawo karshen karya tattalin arzikin da annobar COVID19 ta yi wa Najeriya ta yadda ba'a tsammani.

A wani labarin na daban kuma Hukumar aikin Hajji ta kasa NAHCON ta bayyana cewa yan Najeriya za su samu damar yin aikin Hajji a 2022

Kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da kuma yaɗa labarai na hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Mamoh, yace bana yan Najeriya zasu samu damar sauke farali a kasa mai tsarki.

Prince Mamoh ya bayyyana cewa babu tantama suna da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata zasu gudanar da Hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel