Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

  • Wani jigon jam'iyyar APC, uma tsohon sanata ya riga mu gidan gaskiya a jiya Asabar 20 ga watan Nuwamba
  • Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon sanatan ya yanki jiki ne ya fadi a cikin ofis dinsa, inda aka zarce dashi asibiti
  • Jim kadan bayan zuwa asibiti, majiyoyi sun ce tsohon sanatan ya rasu kuma tsohon dan takarar gwamna ya rasu

Abuja - Tsohon dan takarar gwamna a jihar Ekiti, Sanata Gbenga Aluko ya rasu. An ce dan siyasar haifaffen Ode-Ekiti ya rasu ne a ranar Asabar bayan da ya fadi a ofishinsa da ke Abuja, Punch ta ruwaito.

A cewar Continental Television, an garzaya da shi asibiti inda ya rasu. TVC ta ruwaito cewa daya daga cikin hadiman Aluko da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa Aluko lafiyarsa lau, amma haka dai ya rasu.

Kara karanta wannan

Daliba a jami'ar Umaru Yar’adua ta sha piya-piya don saurayinta ya rabu da ita, an kaita asibiti

Da dumi-dumi: Tsohon sanata ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya
Senator Gbenga Aluko | Hoto: thenationonlineng.net

Wata majiya ta bayyana cewa marigayin dan siyasar ya rasu ne sakamakon bugun zuciya. Ya kasance da ne ga marigayi masanin tattalin arziki, Farfesa Sam Aluko.

Aluko a shekarar 2018 ya tsaya takarar tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Ekiti. Aluko wanda aka fi sani da "SGA" ya kasance dan majalisar tarayya tsakanin 1999 zuwa 2003 a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya wakilci mazabar Ekiti ta Kudu a lokacin.

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

A can baya, shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa, Tribune Nigeria ta ruwaito.

Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Bawa ya tsaya da magana ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa,:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel