Barazanar kora ta daga APC babban abun dariya ne, Sanata Marafa

Barazanar kora ta daga APC babban abun dariya ne, Sanata Marafa

  • Sanata Marafa na jam'iyyar APC ya ce barazanar korar shi daga jam'iyyar babban abun dariya ne kuma ba mafita bace
  • A cewar Marafa, kamata yayi a shawo kan matsalar cikin gida ba wai a sake jagwalgwala matsalar ba ta hanyar korar shi
  • Ya kara da cewa, kwamitin rikon kwaryan an yi shi ne domin zabe ba wai lalata jam'iyyar da suka dade suna ginawa ba

Sanata Kabiru Garba Marafa ya yi fatali da barazanar da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC kan korar shi da suke fadin za su yi sakamakon bayyana abinda ke zuciyarsa.

Ya kwatanta barazanar da lamarin kawai inda yace jam'iyyar ta koma bin doka ko kuma nan babu dadewa bayanta zai zo, Daily Trust ta wallafa.

Barazanar kora ta daga APC babban abun dariya ne, Sanata Marafa
Barazanar kora ta daga APC babban abun dariya ne, Sanata Marafa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Marafa wanda ya taba wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya, a ranar Lahadi ya yi barazanar maka shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar a kotu kan take dokokin da ke kunshe a kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Kwamitin rikon kwaryan ta bakin sakataren ta, Sanata John James a ranar Litinin ya ja kunnen Marafa kan ya mika wuya ga jam'iyyar ko kuma ya fuskanci hukunci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta wallafa cewa, amma a yayin martani, Marafa ya ce ba zai yuwu ya yi shiru ba saboda wannan barazanar ta kwamitin rikon kwaryar ba.

"Kora ta daga jam'iyyar zai sake jagwalgwala lamarin. Babu shakka hakan zai kawo matsaloli, dole ne a mutunta doka.
"Kwamitin nan an yi shi ne ba bisa ka'ida ba kuma ba yadda kundun tsarin mulkin jam'iyya tace ba. Muna gina komai a kan ba komai ba ne. A maimakon barazanar kora ta, kwamitin ko shugaban ta ya fito yayi magana.
"Amfanin kwamitin Mai Mala Buni shi ne shirya zaben jam'iyya. Mai Mala shugaban kwamitin ne ba jam'iyya kadai ba.

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

“Za mu nuna masa hanyar tafiya babu girma balle izza. Ba za mu bar jam'iyyar da muka hada kai muka habaka ba ta lalace a hannun masu son kai da makiyanta ba.
"Wannan jam'iyyar mun dage kan habaka ta, mun saka harsashin nasarar ta. Ba za mu bar wasu kananan mutane su saka son rai tare da lalata ta ba," Sanata Marafa yace.

APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyana matakin da za ta dauka a kan shi

A wani labari na daban, shugabannin jam’iyyar APC sun bukaci shugaban jam’iyyar na reshen jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa da ya yi biyayya ga shugabannin sa ko ya fuskanci hukunci.

Dama Marafa a wani zama na ranar Lahadi a Abuja ya caccaki shugabancin kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar na Gwamna Mai Mala Buni.

Daily Trust ta wallafa cewa, yayin mayar da martani, Darekta janar na harkokin yada labarai ga Gwamna Buni, Mamman Mohammed ya ce:

Kara karanta wannan

Kaduna: Alƙalin kotun shari'a ya ƙwace wa Ibrahim awarwaron da buduwarsa ta bashi don soyayya

“A matsayinsa na dan siyasar da ya san abinda ya ke yi, ya je kotu kawai ya bar surutai da korafi a bayan fage.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel