APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyana matakin da za ta dauka a kan shi

APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyana matakin da za ta dauka a kan shi

  • Shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun bukaci shugaban jam’iyyar na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa da ya yi biyayya ko kuma ya fuskanci hukunci
  • A wani zama da aka yi ranar Lahadi a Abuja, Marafa ya soki shugaban rikon kwaryar jam’iyyar, Gwamna Mai Mala Buni akan yadda ya ke tafiyar da shugabancin jam’iyyar
  • Marafa ya yi barazanar garzayawa kotu don a cire Buni a matsayin shugaban kwamitin rikon kwaryar saboda rashin iya mulki da cancanta

Shugabannin jam’iyyar APC sun bukaci shugaban jam’iyyar na reshen jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa da ya yi biyayya ga shugabannin sa ko ya fuskanci hukunci.

Dama Marafa a wani zama na ranar Lahadi a Abuja ya caccaki shugabancin kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar na Gwamna Mai Mala Buni.

Daily Trust ta wallafa cewa, yayin mayar da martani, Darekta janar na harkokin yada labarai ga Gwamna Buni, Mamman Mohammed ya ce:

Read also

Babbar magana: APC ta yi waje da jigonta saboda ya taya APGA murnar lashe zabe a Anambra

APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyani matakin da za ta dauka a kan shi
APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyani matakin da za ta dauka a kan shi. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC
“A matsayinsa na dan siyasar da ya san abinda ya ke yi, ya je kotu kawai ya bar surutai da korafi a bayan fage.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta wallafa cewa, sai dai a ranar Litinin a Abuja, kakakin bangaren Marafa, Hon. Bello Bakyasuwa ya ce:

“Ba za mu bari surutan kakakin Mai-Mala ya dauke mana hankali ba don mu kawar da ido akan batun da Marafa ya dago.
“Mun ji dadin sa bakin Sanata Marafa ta hanyar garzayawa kotun koli akan rashin yin zaben shugabanni na cikin jam’iyya, daga nan aka fargar da ‘yan siyasan Najeriya inda suka lashi takobin yin abinda ya dace.
“Mun yarda da cewa rashin yin harkokin zabe na gaskiya da gaskiya karkashin mulkinsa su na da alaka da yadda ya tara dukiyar da take da alamar tambayoyi mai dumbin yawa, rashin isasshen ilimin boko don ko digiri ba shi da shi da kuma rashin iya siyasa.

Read also

Rigimar APC ta jagwalgwale a jihar Zamfara, Marafa zai nemi kotu ta tunbuke Mala Buni

“Muna masu bukatar a duba wadannan matsaloli don ba su dace da salon jam’iyyar APC da shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari ba,” a cewarsa.

Sai dai a bangaren Sakataren kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC, Sanata John Monday a wata takarda ta ranar Litinin, ya bukaci Sanata Marafa da ya guji tayar da tarzomar siyasa saboda adawar da ke tsakaninsa da wani, ya kai korafi ga shugabannin jam’iyya don kawo maslaha akan matsaloli.

“Duk wani abu da za a yi a waje ya na nuna rashin tsarin jam’iyya ne, kuma kundin tsarin mulkin APC ya yi magana akan wannan."

Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni

A wani labari na daban, rikicn da ke jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya tsananta a ranar Lahadi yayin da bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa na jam'iyyar a jihar Zamfara suke fara kokarin tsige Gwamna Mai Mala Buni ta hanyar maka shi a kotu.

Read also

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

Buni shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda aka rantsar a watan Yunin 2020, bayan rushe kwamitin NWC karkashin shugabancin Adams Oshiomhole kan zarginsa da yin amfani da kujerarsa ba bisa ka'ida ba, Daily Trust ta wallafa.

Source: Legit.ng

Online view pixel