Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

  • HURIWA ta yi kira ga shugaba Buhari da ya kora, damke tare da gurfanar da Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu kan karyar da yayi a binciken EndSARS
  • Kungiyar ta ce makamanciyar karyar ita ce karyata kisan gillar da Hitler ya yi wa yahudawa wanda tarihi ba za ta manta da shi ba
  • A cewar kungiyar, babu shakka idan Buhari ya kyale Lai Mohammed, hakan zai haifar da kuna a zukatan jama'a wanda har bayan ya sauka daga kujerarsa ba za a manta ba

Kungiyar marubuta masu kare hakkin dan Adam na Najeriya, HURIWA, ta yi kira ga kora, damke tare da gurfanar da ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, kan zarginsa da ake da zabga karya kan abinda ya faru a Lekki tollgate na jihar Legas a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalibin da ya lakadawa lakcararsa duka ya bayyana dalilin dukanta

Kungiyar ta yi ikirarin cewa, ministan ya zuga wa 'yan Najeriya karya inda ta kara da cewa karyarsa ta kawo shubuha a bangaren kwamitin bincike na Legas, The PUNCH ta wallafa.

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga
Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a wata takarda da bayan bayyana sakamakon binciken kwamitin jihar Legas na bin diddigin al'amarin da ya faru a Lekki shekarar da ta gabata.

Duk da Mohammed ya yi ikirarin cewa babu wanda aka kashe, kwamitin ya ce tabbas an kashe mutane masu tarin yawa.

The PUNCH ta ruwaito cewa, rahoton kwamitin ya bayyana yadda aka dinga harbe-harbe da kuma cin zarafin jama'a da 'yan sanda suka dinga, tare da take hakkin bil adama da jami'an tsaro suka dinga yi.

Rahoton mai shafi dari uku da tara ya bada labari dalla-dalla kan yadda sojoji da 'yan sanda suka dinga karantsaye ga dokokin daukar aikinsu a zanga-zangar lumanar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Alƙalin kotun shari'a ya ƙwace wa Ibrahim awarwaron da buduwarsa ta bashi don soyayya

Takardar HURIWA ta ce, "Kamar yadda ya bayyana cewa an dinga cin zarafin farar hula masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate da ke Legas a watan Oktoba, muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayar da umarnin kamawa tare da gurfanar da Lai Mohammed sakamakon karyar da ya dinga yi.
"HURIWA ta na jinjinawa kokarin wadanda suka yi binciken zanga-zangar EndSARS ballantana kan kashe-kashen da sojoji da 'yan sanda suka yi wa jama'a.
“Kungiyar ta na kira ga shugaban kasa da kada ya bar wannan lamarin ya wuce haka kawai, idan kuma ya bar ministan yada labarai da wannan laifin na karyata kashe-kashen nan toh tabbas za a cigaba da tunawa da shi har bayan ya sauka da ga kujerarsa."

EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas

A wani labari na daban, kwamitin binciken da gwamnatin jihar Legas don tattaunawa da wadanda yan sandan SARS suka ci zarafinsu ta sakin rahoton bincikenta kan kashe matasan da akayi ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi zafi, dattawan Arewa sun zauna don neman mafita ga matsalolin Arewa

Kwamitin ta kama jami'an Sojoji da yan sanda da laifin kisa da hallaka matasa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate, jihar Legas ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kwamitin karkashin jagorancin Alkali, Dors Okuwobi, ta gabatar da rahotonta ga ofishin Gwamnan jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel