Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

  • Rahotannin da suke iso mu sun shaida cewa, dalibin da ya daki malamarsa a jami'ar Ilorin ya samu takardar kora
  • Hukumar jami'ar ta bayyana korar dalibin ne bayan da ya amsa cewa, ya lakadawa malamar tasa duka saboda wasu dalilai
  • A wata hira dashi, ya bayyana yadda ya bibiyi malamar domin ta taimaka masa a shirin SIWES da yake yi

Ilorin, Kwara - Hukumar gudanarwar jami’ar Ilorin ta kori wani dalibi mai suna Salaudeen Waliu Aanuoluwa na tsangayar nazarin ilmin halittu, bayan da aka same shi da laifin cin zarafin wata malamar jami’ar, Misis Rahmat Zakariyau.

A baya mun kawo muku rahoton yadda dalibin jami'ar dan aji hudu ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka a harabar jami'ar saboda kin taimakonsa.

Wata sanarwa da Daraktan hulda na Jami’ar, Mista Kunle Akogun, ya fitar, ta bayyana cewa kwamitin ladabtarwa na dalibai ne ya yanke hukuncin.

Da dumi-dumi: Jami'a ta kori dalibin da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka
Jami'ar Ilorin ta kori dalibinta | Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

Hakazalika an gurfanar da Salaudeen a ranar Litinin ga kwamitin, inda Akogun ya kara da cewa “yana da kwanaki 48 don daukaka kara kan hukuncin da aka yanke daga shugaban jami'ar idan ya ji bai gamsu da hukuncin ba”.

Jaridar Punch ta ruwaito Akogun na cewa:

"Tun daga lokacin aka mika Salaudeen ga 'yan sanda domin daukar matakin da ya dace."

Wasikar korar Salaudeen ta fito ne daga ofishin magatakardan jami'ar ta Ilorin.

A wani rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Daily Trust, dalibin ya bayyana dalilin da yasa ya sa hannu ya daki malamar tasa.

A cewarsa, malamar tasa ce ta fara jifansa da kofin shan shayi, lamarin da ya tunzura shi har ya dauki matakin da bai dace ba.

Daga alamun kalamansa, Salaudeen ya nuna nadama da aikata wannan mummunan aiki.

Wani dalibin jami'a ya lakadawa malamarsa duka kawo wuka daga neman taimako

A baya kunji cewa, dalibi dake karantar kwas din Microbiology a jami'ar Ilorin, (UniLorin) ya lakadawa lakcaransa mace dukan kawo wuka.

Daily Trust tace dalibin mai suna, Captain Walz, bai samu damar yin kwas din neman sanin makamar aiki ba (SIWES), dan haka yaje neman taimakon lakcaran.

Rahotanni sun bayyana cewa lakcaran da abin ya shafa, Mrs Zakaria, ita ce zata kula da dalibin yayin da zai yi Project a 400 level.

Asali: Legit.ng

Online view pixel