Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni

Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni

  • Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC na cigaba da kamari yayin da bangaren Sanata Kabiru Marafa suka tashi tsaye wurin ganin an tsige Buni
  • Kamar yadda Marafa ya bayyana, ba a taba zaben Buni ba a matsayin shugaban jam'iyyar ba kuma kundin tsarin mulki bai aminta da hakan ba
  • Marafa ya ce za su yi amfani da kotu wurin tsige Buni domin ya na dakile duk wani cigaban jam'iyyar a reshen ta na jihar Zamfara

Abuja - Rikicn da ke jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya tsananta a ranar Lahadi yayin da bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa na jam'iyyar a jihar Zamfara suke fara kokarin tsige Gwamna Mai Mala Buni ta hanyar maka shi a kotu.

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

Buni shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda aka rantsar a watan Yunin 2020, bayan rushe kwamitin NWC karkashin shugabancin Adams Oshiomhole kan zarginsa da yin amfani da kujerarsa ba bisa ka'ida ba, Daily Trust ta wallafa.

Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni
Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamitin ya gaza, daga cikin wasu abubuwa, yin taron zaben shugabannin jam'iyya. Wannan cigaban ya kawo rikici tare da hargitsi tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Abuja, Sanata Marafa ya ce Buni ya shirya tsaf domin tarwatsa jam'iyyar inda ya kara da cewa gwamnan ba shi da gogewar shugabancin jam'iyyar a shari'ance.

Ya ce bangarensa za su kalubalanci Buni a kotu a matsayinsa na gwamna mai ci a yanzu kuma shugaban APC a lokaci daya, akasi ga tanadin kundin tsarin kasar nan na 1999.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya sake barkewa tsakanin 'yayan jam'iyyar APC a jihar Zamfara

Marafa ya ce ba a taba zabensa a matsayin shugaban jam'iyya ba ta hanyar gangami, taron jam'iyya ko zabe, akasi da sashi takarda ta 17 a kundin tsarin mulkin APC.

Ya ce kwamitin Buni na zagon kasa ga kokarin masu ruwa da tsaki wurin dawo da zaman lafiya a jam'iyyar, reshen jihar Zamfara.

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

A wani labari na daban, Idan za a tuna, zaen shugabannin jam'iyya na yankin arewa maso yamma an dakatar da shi bayan rikicin da bangaren tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da na tsohon ministan al'amuran waje, Ambasada Aminu Wali suka fara kan mukamin mataimakin shugaban jam'iyya.

Daily Trust ta wallafa cewa, mukamin wanda aka ayyana dan jihar Kano ne zai samu, ya tada kura tsakanin bangarorin biyu masu fatan cafke mukamin domin kara musu haske a shekarar 2023.

Mukaman 17 na yankuna sun hada da manyan mukamai 7 wadanda za a rarrabe tsakanin jihohi 7 na arewa. Jihohin sun hada da Jigawa, Kaduna, Katsina, Kano, Kebbi, Sokoto da Zamfara.

Kara karanta wannan

Buhari Baya nan: Sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC ta kasa, Mala Buni ya shiga tasku

Asali: Legit.ng

Online view pixel