Rigimar APC ta jagwalgwale a jihar Zamfara, Marafa zai nemi kotu ta tunbuke Mala Buni

Rigimar APC ta jagwalgwale a jihar Zamfara, Marafa zai nemi kotu ta tunbuke Mala Buni

  • Sanata Kabiru Garba Marafa ya sha alwashin kai karar kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC kotu
  • A cewar Kabiru Garba Marafa, Mai Mala Buni bai cancanta ya rike APC yayin da yake Gwamna ba
  • Jigon na APC ya zargi Buni da kawo fitina a jam'iyya, yace shugabancin rikon da yake yi, ya saba doka

Abuja Jaridar Daily Trust tace sabanin da ya shiga tsakanin ‘ya ‘yan APC a jihar Zamfara ya kara cabewa a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, 2021.

Bangaren Sanata Kabiru Garba Marafa a jam’iyyar APC tace za ta nemi kotu ta tsige Gwamna Mai Mala Buni daga kujerar shugaban rikon kwarya na kasa.

Tsohon Sanatan Zamfara, Kabiru Garba Marafa ya zanta da ‘yan jarida a Abuja, inda yace gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya zo ne ya rikita APC.

Kara karanta wannan

Babbar magana: APC ta yi waje da jigonta saboda ya taya APGA murnar lashe zabe a Anambra

Nadin kwamitin Mai Mala Buni ya saba doka?

A cewar Kabiru Marafa, Mala Buni bai cancanta ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa ba.

Jaridar tace Marafa ya kafa hujja da kundin tsarin mulki na kasa da dokar APC, wadanda yace duk ba su halattawa gwamna ya jagoranci ragamar jam’iyya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan siyasar yace babu yadda za ayi Buni ya zama shugaban jam’iyya ba ta hanyar gangami ko zabe ba, kamar yadda sashe na 17 (4) na dokar APC tayi tanadi.

Mala Buni
Muhammadu Buhari da Mai Mala Buni Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Mala Buni ya kawo matsaloli ne a APC - Marafa

Har ila yau, Sanata Marafa ya zargi kwamitin rikon kwarya na Mala Buni da kawo cikas wajen kokarin sulhunta ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a reshen jihar Zamfara.

“Ba mu nemi rigimar kowa ba, mun yi kokarin mu tafi da wadanda suka shigo (Gwamna Matawalle), amma jam’iyya ta fusata mu.” - Kabiru Marafa

Kara karanta wannan

Babban darasin da APC ta koya a zaben Gwamnan Anambra inji Tsohon Hadimin Buhari

Gwamna Mala Buni ya yi wa Matawalle martani

Da aka tuntubi Darekta Janar na yada labarai da hulda da jama’a na gwamna Buni, Alhaji Mamman Mohammed yace Marafa ya tafi kotu, ya daina surutu.

“A matsayinsa na ‘dan siyasar da ya san abin da yake yi, ya tafi kotu kawai, kar ya zama shi ne mai kara, kuma shi ne Alkalin.” – Mamman Mohammed.

Mohammed yace babatun banza Marafa yake yi a game da zabuka da shugabancin APC, yana kuka ne kawai saboda an yi zabe, kuma bangarensa sun sha kashi.

PDP ta ba Arewa tikiti a zaben 2023

A yau aka ji wani jigon jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, ya bayyana cewa wajibi ne jam'iyyar PDP ta kai takarar shugaban ƙasa zuwa yankin Arewacin Najeriya a 2023.

Lawal Usman, wanda aka fi sani da Mista LA, yace yana da manyan dalilan faɗin haka matukar jam'iyyar tana son komawa kan mulkin da ta rasa tun a zaben 2015.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya tsananta yayin da bangaren Marafa ke kokarin tsige Mai Mala Buni

Asali: Legit.ng

Online view pixel