Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1

Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1

  • Misis Eunice Ngozi Onuegbusi daga karamar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra ta zama attajira
  • Hakan ya kasance ne bayan matar ta ki yarda ta siyarwa wakilan yan siyasa kuri’arta a lokacin zaben Anambra
  • Gwamna Obiano ya yi mata kyautar naira miliyan 1 saboda biyayyar da ta nunawa jam’iyyarsa ta APGA

Awka, Jihar Anambra Gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya yiwa wata mata mai suna Misis Eunice Ngozi Onuegbusi kyautar zunzurutun kudi har naira miliyan 1.

Misis Onuegbusi, mutuniyar Ukwulu (kauyen Magu) Ward 1, rumfar zabe ta 04 a karamar hukumar Dunukofia da ke jihar, ta ki amsar N5,000 daga wakilin wata jam’iyya a yayin zaben gwamnan Anambra da aka kammala.

Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1
Zaben gwamnan Anambra: Obiano ya yiwa matar da ta ki siyar da kuri’arta kyautar miliyan N1 Hoto: Amb Adichie Izuchukwu
Asali: Facebook

A cikin wani bidiyo da ya karade yanar gizo, an gano yadda Madam Eunice ta ki amsar N5,000 daga wakilin wata jam’iyya a rumfar zabenta a lokacin zaben na ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da suka ba Farfesa Soludo da APGA gudumuwa a zaben Gwamnan Anambra

Maimakon haka ta ce lallai ita jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) za ta jefa wa kuri’arta.

Da yake magana a wani taron coci inda ya sanar da kyautar, Gwamna Obiano ya ce:

"Duk da cewar Madam Eunice ta san cewa kudi zai bata nutsuwar zuciya na dan lokaci kadan, ta san cewa Anambra zai fi inganta idan ta zabi abun da ranta yake so.
"Na maza da matan jam'iyyarmu masu kishi ne, wadanda suka bijirewa kwadayin kudi daga jam'iyyun hamayya don taya APGA yaki saboda sun san cewa nasarar APGA nasarar talakawan wannan jiha ta mu ne.
"Sannan daga karshe, na al'umman Anambra da ke gida da waje ne, wadanda suka tsaya tsayin daka a bayan APGA ba wai don mun cika dukka abubuwan da mutane suka yi tsammani bane illa saboda ginshikin da ni da tawagata muka shimfida zuwa yanzu, sun ga isasshen haske da ke nuna cewa jihar Anambra tamkar rana ce da za ta iya haskowa, a cikin kowani yanayi. kuma wannan ne dalilin da yasa muka lashe wannan zabe."

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Tambuwal ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa

Zaben Anambra 2021: Shugaba Buhari na daban ne wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Najeriya, Dan majalisa

A wani labarin, dan majalisar dokokin jihar Legas, Jude Idimogu, yace shugaba Buhari na daban ne wajen tabbatar da sahihin zabe a Najeriya.

Daily Nigerian tace Ɗan majalisan ya yi wannan furuci ne yayin da yake tsokaci kan zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka kammala cikin nasara.

Mista Idimogu, wanda ya shafe zango biyu yana wakiltar mazaɓar Oshodi-Isolo ta II a majalisar dokokin Legas, ya shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa Buhari ba ya katsalandan a ɓangaren zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel