Abubuwa 6 da suka ba Farfesa Soludo da APGA gudumuwa a zaben Gwamnan Anambra

Abubuwa 6 da suka ba Farfesa Soludo da APGA gudumuwa a zaben Gwamnan Anambra

  • Farfesa Charles Chukwuma Soludo ne ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra da aka yi kwanan nan.
  • Tsohon gwamnan na CBN ya doke ‘yan takara irinsu; Andy Uba, Ifeanyi Uba da Valentine Ozigbo.
  • APGA tayi shekara 14 tana mulki a jihar Anambra, akwai yiwuwar ta cigaba da rike jihar har zuwa 2025.

Jaridar Daily Trust ta tattaro wasu dalilan da suka taimakawa jam’iyyar APGA wajen samun nasara a zaben. Mun kawo maku wasu daga cikin wadannan dalilai:

1. Karfin jam’iyyar APGA

APGA da aka kafa a shekarar 2003 take rike da jihar Anambra tun 2006. Jam’iyyar tayi karfi a jihar ta yadda za ta iya doke duk ‘dan takarar da wata jam’iyya ta tsaida.

2. Karfin gwamnati

Gwamna Willie Obiano ya ba gudumuwa sosai a wannan zabe kamar yadda Peter Obi ya taimaka masa a 2014. Magoya baya da dukiyar Obiano sun yi wa Soludo tasiri.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya amince da shan kaye, ya taya Soludo murna

3. Ilmin boko

Farfesa Charles Chukwuma Soludo mutum ne mai matukar ilmi, masanin tattalin arziki ne wanda ya kai matsayin Farfesa. Wannan ya taimaka masa a wannan zaben.

Zaben Gwamnan Anambra
'Yan takarar Gwamna a Anambra Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

4. Sabanin addini

Rahoton na Daily Trust tace ra’ayin addini ya taimakawa APGA a zaben. Charles Chukwuma Soludo mabiyan katolika ne wanda sun fi mabiya angilikan yawa a Jihar.

5. Muhawarar da aka yi

An shiryawa ‘yan takara muhawara wajen zaben sabon gwamna a jihar Anambra, wanda ya ba masu kada kuri’u damar sanin ‘dan takarar da ya fi kamata su zaba.

6. Tanadi

Charles Chukwuma Soludo ya dade yana shirin zama gwamnan jihar Anambra. Tsohon gwamnan bankin na CBN yace ya fi shekara 18 yana jiran wannan rana.

7. Jami’an tsaro

Ana kyautata zaton cewa jami’an tsaro sun bada gudumuwa a zaben. An baza ‘yan sanda da sojoji saboda tsoron dakarun kungiyar IPOB su kawo matsala a yankin.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

Gwamnatin Amurka ta yaba

A ranar Laraba ne Gwamnatin kasar Amurka ta yaba da yadda INEC ta gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra, tace ra'ayin mutane ya yi tasiri a zaben.

Gwamnatin Amurka ta bayyana wannan ne a wani jawabi da ta fitar ta bakin ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel