2023: Gwamna Tambuwal ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa

2023: Gwamna Tambuwal ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa

  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya magantu a kan ko zai tsaya takarar shugaban kasa a babban zaben 2023
  • Tambuwal ya bayyana cewa a yanzu abun da ya fi mayar da hankali a kai shine yadda za su saisaita jam'iyyarsu ta PDP domin ta tsaya da kafafunta kafin zaben
  • Ya kuma bayyana cewa yana tuntuba a yanzu amma zai sanar da hukuncinsa da zaran ya kammala

Jihar Sokoto - Yayin da ake ci gaba da tattauna batun wanda zai gaji kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya magantu a kan ko zai tsaya takarar kujera ta daya a kasar.

A wata hira da yayi da jaridar Premium Times, Tambuwal wanda shine shugaban gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa abun da suka fi mayar da hankali a kai a yanzu haka shine yadda za su daidaita babbar jam’iyyar adawar kasar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kawo dabarar hana magudin zabe, za a rika aiki da na’ura wajen tattara kuri’u

2023: Gwamna Tambuwal ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa
2023: Gwamna Tambuwal ya bayyana matsayarsa kan takarar kujerar shugaban kasa Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa yana so abubuwan su kankama a jam’iyyar kafin ya ayyana aniyarsa a kan babban zaben kasar mai zuwa ta 2023.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kun san cewa a wannan lokaci, muna ta kokarin ganin cewa mun daidaita jam’iyyar. Idan jam’iyyar bata hadu sannan ta daidaita ba, wani kudiri mutum zai kasance da shi? Dole sai kana da jam’iyya kafin ka yi Magana kan kudirinka. A yanzu da muka kusa kammala dukka tarukanmu, zan dawo gare ku bayan na gama tuntuba a yan makkwanni ko watanni kadan masu zuwa.
“Na gwada a baya. Shi (kudirin shugabancin kasa) ya kasance a iska a 2014. Bayan tuntuba, na yanke shawarar tsayawa takarar. A 2018, bayan tattaunawa da wasu masu ruwa da tsaki sai na yi watsi da tsayawa tseren. Zan fara tattaunawa a yanzu sannan zan bayyanawa duniya sakamakon bayan nan."

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Jami'an tsaro da 'yan IPOB sun shafe sa'o'i uku suna musayar wuta

2023: Abin da jam'iyyar PDP za ta yi idan APC ta tsayar da Jonathan matsayin ɗan takara, Tambuwal

A gefe guda mun ji cewa a baya-bayan nan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta musanta jita-jitar da ake yadawa cewa tana shirin tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar ta a 2023, amma har yanzu ana tattaunawa kan batun.

Gwamnan na jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya kuma bayyana dalilan da yasa tsohon shugaban kasa Jonathan bai hallarci babban taron jam'iyyar PDP na kasa ba da aka yi kwanan nan.

A cewar Tambuwal, Jonathan yana da wani taron da zai hallarta a kasar Kenya, don haka jam'iyyar ta bashi izini ya tafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel