Abinda Ya Dace Yan Najeriya Su Yiwa Shugabannin da Suka Gaza Cika Alkawari, Tsohon Ministan Sadarwa
- Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana, ya shawarci yan Najeriya kan matakin da ya dace su ɗauka kan shugabannin da suka gaza
- Gana ya bayyana cewa yan Najeriya suna da wuka da nama a hannunsu wajen zaɓar wanda suke so ya jagorance su
- Jigon PDP ya yi kira ga mutane su tashi tsaye kuma su tabbatar an yi ingantaccen zaɓe a 2023
Abuja - Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Jerry Gana, yace ya kamata yan Najeriya su canza shugabanni da jam'iyyun siyasar da basu taɓuka komai a zaɓen 2023, kamar yadda This Day Live ta ruwaito.
A cewarsa, maimakon da nasani da bacin rai, kamata yayi yan Najeriya su saurari lokacin da ya dace a babban zaɓen dake tafe don hukunta shugabannin da suka gaza cika alkawurransu.
Gana ya faɗi haka ne a wata fira da manema labarai jim kaɗan bayan kaddamar da sabuwar cocin Anglican a Zone 5, Wuse Abuja, ranar Lahadi.
Gwamnati ta gaza cika alkawarinta kan tsaro
Da yake magana dangane da karuwar kalubalen tsaro a Najeriya, Farfesa Gana yace:
"Ya kamata yan Najeriya su kalli lamarin dake faruwa yanzu a matsayin gwamnati ta gaza cika alƙawurran da ta ɗauka musamman kan tsaro."
"Yanayin tsaron da ake ciki babban abin damuwa ne, amma kamata ya yi mutane su kalli abun a tsarin demokaradiyya. Su kalli abin da cewa alkwarin da wannan gwamnatin ta ɗauka ta gaza."
"Sabida haka su shirya wa babban zaɓe mai zuwa kuma kada su cika sanya wa kansu damuwa domin zaɓe hanya ce ta canza shugabanni, yan Najeriya na da damar zaɓan waɗanda zasu yi abinda ake bukata."
Sai mutane sun tashi tsaye wajen zaɓe
Da yake magana kan tsarin zaɓe a ƙasar nan, tsohon ministan ya yi kira ga al'umma su tashi tsaye wajen tabbatar da sun zaɓi shugabanni nagari a 2023.
Jigon PDP yace bai dace yan Najeriya su karaya ba, kuma su tashi tsaye wajen tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A wani labarin kuma Mataimakin Gwamna Ya Yi Magana Kan Shirinsa Na Ficewa Daga Jam'iyyar PDP
Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu, ya bayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da uban gidansa, Gwamna Obaseki.
Shaibu ya faɗi cewa tabbas akwai matsalolin dake faruwa a cikin PDP, amma bai shafi alakarsa da gwamna ba.
Asali: Legit.ng