Da duminsa: An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun hana Sanatan APGA shiga garin

Da duminsa: An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun hana Sanatan APGA shiga garin

  • Jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun mamaye karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra domin kammala zaben gwamnoni
  • Sojoji sun tare jigon APGA kuma Sanata mai wakiltar Anambra ta tsakiya, Victor Umeh tare da hana shi shiga karamar hukumar
  • Duk kokarin da yayi domin yi musu bayani, sun ce babu dalilin da zai sa su bar shi shiga cikin garin da ake zaben a yau Talata

Ihiala, Anambra - Tsaro ya tsananta a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra inda ake karasa zaben jihar Anambra a yau Talata, Daily Trust ta wallafa.

Sojoji sun hana Sanata Victor Umeh, wakilin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar daga shiga karamar hukumar Ihiala yayin da aka tura jami'an INEC.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba

Da duminsa: An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun tare jigon APGA
Da duminsa: An tsananta tsaro a Ihiala ta Anambra, sojoji sun tare jigon APGA. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A tare da wasu magoya bayansa da hadimansa, Umeh, wanda ya kwana a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke Awka yayin da ake tattara sakamakon kananan hukumomi 21 na jihar, an wartake sa daga shiga garin Ihiala.

Wani babban jami'in soja ya sanar da Sanatan mai wakiltar Anambra ta tsakiya a majalisar dattawa cewa ba zai iya shiga garin ba.

Dukkan kokarin babban dan siyasan na sanar da dalilinsa na shiga garin, sojojin sun jajirce tare da hana shi shiga, Daily Trust ta wallafa.

Hukumar zabe ta bayyana zaben Anambra matsayin Inconclusive

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana zaben jihar Anambra a matsayin wanda bai kammalu ba.

Farfesa Comfort Obi, baturiyar zaben a jihar, ta ce ba za su iya bayyana wanda ya ci zaben ba saboda ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala da ke jihar ba wacce ke da mutum 148,487 da INEC ta yi wa rijista.

Kara karanta wannan

Da duminsa: INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin 'Inconclusive'

Akwai tazarar kuri'u 52,624 tsakanin Farfesa Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA wanda ya samu kuri'u 103,946 da kuma Valentine Ozigbo na jam'iyyar People Democratic Party’s (PDP) wanda ya samu kuri'u 51,322.

Zaben Anambra: Abubuwa 8 muhimmai da suka faru a yayin zaben

A wani labari na daban, Gagarumin zaben gwamnonin da ake ta jira ya faru a jihar Anambra ya auku a ranar Asabar, kamar yadda aka tsara. Sai dai har yanzu ba a kammala zaben ba balle a sanar da dan takarar da ya lashe zaben.

Dangane da wadanda su ke ta mamaki akan abubuwan da su ka auku cikin kwanakin na karshen mako kuma da dalilin da ya sa ba a sanar da wanda ya ci nasara ba, akwai abubuwa 8 da ya kamata su sani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel