Da duminsa: INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin 'Inconclusive'

Da duminsa: INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin 'Inconclusive'

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin zaben da bai kammala ba, wato Inconclusive
  • Baturiyar zaben jihar, Farfesa Florence Obi, ta bayyana hakan a ofishin hukumar da ke garin Awka a jihar Anambra
  • Sai dai, ta tabbatar da cewa, Farfesa Chukwuma Soludo ne ke da kuri'u mafi rinjaye a jimillar sakamakon zaben da aka samu yanzu
  • Florence ta sanar da cewa, za a yi zaben karamar hukumar Ihiala a ranar Talata mai zuwa sannan a cigaba da sanar da sakamako

Awka, Anambra - Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Anambra a matsayin wanda bai kammalu ba, Daily Trust ta wallafa.

Farfesa Florence Obi, baturiyar zaben jihar, ta sanar da hakan ne a ofishin hukumar INEC da ke Awka, babban birnin jihar Anambra a sa'o'in farko na ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Da duminsa: INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin 'Inconclusive'
Da duminsa: INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin 'Inconclusive'
Asali: Original

Ta ce ba za a iya bayyana wanda yayi nasarar zaben ba saboda ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala ta jihar.

A yayin kare abinda suka aikata da dokar zabe, Obi ta ce za a yi zaben maye gurbi a karamar hukumar Ihiala a ranar Talata.

"Ni, Farfesa Florence Obi, da karfin ikon da aka bani na matsayin baturiyar zabe, na dakatar da tattarawa tare da sanar da sakamakon kowanne zabe har sai an yi zabe a rumfuna 320 da ke karamar hukumar Ihiala."
"Zaben da za a yi, za a yi shi ne a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba," tace.

Farfesa Chukwuma Soludo na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ne ya samu kuri'un da suka fi na kowa yawa a zaben ranar Asabar, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Ba a yi zabe a Ihiala ba: An dage zaben gwamna a wata karamar hukuma saboda matsala

A yayin sanar da dukkan kuri'un da 'yan takara suka samu, Obi ta ce Soludo ya samu kuri'u 103,946, Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri'u 51,322, yayin da Sanata Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri'u 42,942.

An samu mutum 246,638 da aka yi musu rijistar zaben yayin da aka tantance masu kada kuri'a 241,090.

An saka kuri'u masu amfani 229,521 inda wasu 7,841 suka lalace. An kada jimillar kuri'u 237,362 a zaben.

Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

A wani labari na daban, akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin jihar da ke Awka a jihar Anambra.

Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zabe a kananan hukumomi sama da biyu bisa uku na jihar, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Rahoto: INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zabe a wasu rumfuna a zaben Anambra

Sanata Ifeanyi Uba na jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi nasarar lashe kananan hukumomi daddaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel