Zaben Anambra: Abubuwa 8 muhimmai da suka faru a yayin zaben

Zaben Anambra: Abubuwa 8 muhimmai da suka faru a yayin zaben

  • An yi fitaccen zaben da aka dade ana labari ranar Asabar kamar yadda aka shirya za a yi a jihar Anambra duk da manyan kalubale
  • Sai dai zaben bai kammalu ba kamar yadda ya kamata, kuma ba a sanar da zababben gwamnan jihar ba
  • Ga wadanda suke mamakin abinda ya faru, ga abubuwa 8 da ke a kasa a halin yanzu da kuma abinda ake jira zai iya faruwa

Anambra - Gagarumin zaben gwamnonin da ake ta jira ya faru a jihar Anambra ya auku a ranar Asabar, kamar yadda aka tsara.

Sai dai har yanzu ba a kammala zaben ba balle a sanar da dan takarar da ya lashe zaben.

Dangane da wadanda su ke ta mamaki akan abubuwan da su ka auku cikin kwanakin na karshen mako kuma da dalilin da ya sa ba a sanar da wanda ya ci nasara ba, akwai abubuwa 8 da ya kamata su sani:

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zabe ba

Zaben Anambra: Abubuwa 8 muhimmai da suka faru a yayin zaben
Zaben Anambra: Abubuwa 8 muhimmai da suka faru a yayin zaben
Asali: UGC

1. An yi zaben Anambra cikin kwanciyar hankali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ganau su ka bayyana, an yi zaben cikin lumana. Dangane da yadda gaba daya zaben ya kasance, komai ya tafi yadda aka tsara.

2. Masu zabe sun fito

Masu zabe sun fito. Dangane da zaben ranar Asabar, duk da farko mutane a firgice su ke amma abin ya tafi cikin lumana.

Duk da dai mutanen da su ka kula da zaben sun ce ba tururuwa aka dinga wurin fitowa zaben ba, amma mutane sun fito sun nuna ra’ayin su.

Sannan har ‘yan jarida sun bayyana don su dauki rahotanni akan abubuwan da su ke faruwa babu wani tsoro.

3. An samu isassun matakan tsaro

An aike jami’an tsaro kamar ‘yan sanda, sojoji da sauran su don tabbatar da tsaron yankin.

Sai dai akwai jami’an tsaron da su ka ce ba a biya su kudaden ayyukan da su ka yi ba wanda hakan ya ci karo da sanarwar da hukumar ‘yan sanda ta yi.

Kara karanta wannan

Ba a yi zabe a Ihiala ba: An dage zaben gwamna a wata karamar hukuma saboda matsala

4. An yi ta siyan kuri’u

Yayin da ake zabe, kungiyar NCS da CDD sun amince da cewa an siya kuri’u a wuraren akwatunan zabe da ke jihar.

Sun bayyana yadda jama’a su ka dinga siyar da kuri’ar su daga N1,000 zuwa 6,000 a wurare daban-daban.

Sai dai kamar yadda kungiyoyin su ka bayyana, ba bainar jama’a aka yi ba, cikin sirri komai ya faru.

5. An samu ‘yan matsaloli

An samu matsaloli dangane da zaben shi kan shi kuma Hukumar INEC ta shaida hakan.

Hukumar ta bayyana yadda wasu daga cikin injinan da aka yi ayyukan zaben su ka ki yin aiki yayin da wasu wuraren ba su samu kayan aiki ba.

6. Ma’aikatan zaben sun tsere da takardun sakamakon zabe

An yi zaben Anambra cikin lumana fiye da tunanin mai rai.

Sai dai ma’aikatan zaben sun tsere da sakamakon zabe na wurare 41 a Oba 2, karamar hukumar Idemili ta kudu da ke jihar.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Jami’in zaben mai alhakin tattara sakamakon zaben na karamar hukumar, Gabriel Odoh ya ce ma’aikatan zabe sun tsere da sakamakon zabe na wurare 41.

Duk da dai bai bayyana sunayen ma’aikatan ba. Ya kuma bayyana yadda aka kwace akwatin zabe a Oba 1.

7. Soludo ne ya ci zaben kananun hukumomi 19 cikin 21

Dan takarar gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APGA, Charles Soludo ya lashe zabe a kananun hukumomi 19 wadanda aka bayyana sakamakon su.

Daga shi sai dan takarar jam’iyyar PDP, Valentine Ozigbo, tukunna dan takarar YPP, Sanata Ifeanyi Ubah wanda ya lashe zaben karamar hukuma daya.

Sai dai dan takarar APC, Sanata Andy Uba bai samu nasara a ko da karamar hukuma daya ba.

8. Za a sake zaben Ihiala a ranar Talata

Jami’ar da ke da alhakin kula da zaben jihar, Farfesa Florence Obi ta ce za a sake zabe a Ihiala saboda rashin tsaron yankin a ranar Talata, 9 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: IGP ya bukaci sunayen 'yan sandan da har yanzu ba a biya ba a Anambra

Ta bayyana yadda hukumar zaben ta ke shirin tura kayan aiki ga ma’aikatan a karamar hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel