Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba

Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba

  • Bayan hutun kwana biyu sakamakon rashin cikashe zaben Anambra, yau za'a cigaba daga inda aka tsaya
  • Charles Soludo na jam'iyyar APGA ke kan gaba inda ya lashe kuri'un kananan hukumomi 17
  • Dan takaran Jam'iyyar PDP ke biye da shi da kuri'u 51322, sai kuma jam'iyyar APC mai jimillan kuri'u 42942

Awka - Hukumar gudanar da zaben kasa watau INEC ta bayyana cewa zaben jihar Anambra da aka cikashe yau Talata zai gudana ne tsakanin karfe 10 na safe zuwa 4 na rana.

Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan jama'a na INEC, Festus Okoye, ya sanar da hakan bisa jawabin da ya saki ranar Litinin.

Yau a karamar hukumar Ihiala zabe zai gudana.

Read also

Zaben Anambra 2021: Akwai sauran rina a kaba, inji dan takarar PDP, Valentine

Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba
Zaben Anambra: Yau Talata za'a cigaba daga inda aka tsaya, APGA na kan gaba
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaku tuna cewa hukumar INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Anambra a matsayin wanda bai kammalu ba.

Farfesa Florence Obi, baturiyar zaben jihar, ta sanar da hakan ne a ofishin hukumar INEC da ke Awka, babban birnin jihar Anambra a sa'o'in farko na ranar Litinin.

Ta ce ba za a iya bayyana wanda yayi nasarar zaben ba saboda ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala ta jihar.

A yayin kare abinda suka aikata da dokar zabe, Obi ta ce za a yi zaben maye gurbi a karamar hukumar Ihiala a ranar Talata.

Tace:

"Ni, Farfesa Florence Obi, da karfin ikon da aka bani na matsayin baturiyar zabe, na dakatar da tattarawa tare da sanar da sakamakon kowanne zabe har sai an yi zabe a rumfuna 320 da ke karamar hukumar Ihiala."

Read also

Zaben Anambra: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zabe ba

Ya sakamakon zaben yake yanzu?

A yanzu, jimillan sakamakon zabe da kuri'in da kowace jam'iyya ta samu da hukumar INEC ta sanar a kananan hukumomi 19 shine:

A— 1793

AA— 76

AAC— 580

ADC— 313

ADP— 743

APC— 42942

APGA— 103946

APM— 288

APP— 133

BP— 173

LP— 2697

NNPP— 111

NRM— 207

PDP— 51322

PRP— 428

SDP— 782

YPP— 20917

Source: Legit.ng

Online view pixel