Ba a yi zabe a Ihiala ba: An dage zaben gwamna a wata karamar hukuma saboda matsala

Ba a yi zabe a Ihiala ba: An dage zaben gwamna a wata karamar hukuma saboda matsala

  • A yayin da ake ci gaba da sanar da sakamakon zabe a jihar zaben da ya gudana a jihar Anambra, hukumar INEC ta dage zaben wani yanki
  • An dage zabe a karamar hukumar ta Ihiala ne sakamakon wata matsala da aka samu a wasu yankunan karamar hukumar
  • Har yanzu ana ci gaba da karbar sakamakon zabe, kuma jami'an tattara zabe na bayyana abubuwan da suka faru a rumfunan zabe

Anambra - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage zaben gwamna a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra sakamakon wasu kura-kurai da aka gano a yankin.

INEC ta dage zaben ne zuwa ranar Asabar 13 ga watan Nuwamba, 2021, inda ta gargadi masu tayar da zaune tsaye da su kaucewa duk wuraren da za a gudanar da zaben a karamar hukumar Ihiala.

Kara karanta wannan

Rahoto: INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zabe a wasu rumfuna a zaben Anambra

Da duminsa: An dage zaben gwamna a wata karamar hukuma saboda matsala
Hukumar INEC ta dage zabe | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ce ta ziyarci wasu wuraren da ake gudanar da zaben, ciki har da makarantar firamare ta Okohia Ihiala amma ta jami’an INEC da za su gudanar da zaben, inda suka kwashe kayansu domin barin wurin.

Kokarin tattaunawa da jami’an hukumar ta INEC da ke makarantar firamare ta Okohia Ihiala ya ci tura yayin da suka yi ikirarin cewa ba su da ikon yin magana a kan lamarin amma sun bayyana cewa an dage zaben zuwa ranar Asabar mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai da aka tuntubi kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar Anambra, C Don Adinuba, ya ce wani fitaccen dan siyasa a yankin da tawagarsa sun kitsa murde zaben bayan kammala wani shiri makamancin haka a wasu yankunan na Ihiala.

Ya kara da cewa, jami’an tsaro sun kama wasu daga cikinsu kuma sakamakon rudanin da ya biyo baya, INEC ta dage zaben.

Kara karanta wannan

Zuwa yanzu INEC ta karbi sakamakon zaben kananan hukumomi 19 cikin 21

Adinuba ya yi alfaharin cewa, ko menene ‘yan siyasar da ke son yin magudin zabe a karamar hukumar Ihiala za su yi, jam'iyyar APGA za ta lashe a ranarAsabar domin sun fi sauran jam’iyyun siyasa mutane.

Jami'in tattara sakamakon zabe ya ce, duk da yawan masu jefa kuri'u a yankin, amma ba a yi zaben ba, The Cable ta ruwaito.

Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

A wani labarin, jam’iyyar APGA ta lallasa jam'iyyar tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, da Sanata Uche Ekwunife, a karamar hukumarsu, This Day ta ruwaito.

Dukansu ‘yan karamar hukumar Anaocha ne, kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Shi ma dai Sanata Victor Umeh ya fito daga karamar hukumar.

Dokta Okene Isaac, malami a Jami’ar Calabar, wanda shi ne jami’in tattara bayanan kananan hukumomi ya ce: “Jimillar masu kada kuri’a 109860, sun amince da kada kuri'u 15940."

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Anambra: DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel