Zaben Anambra: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zabe ba

Zaben Anambra: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zabe ba

  • Duk da hada sakamakon zabe a kananan hukumomi 19 daga cikin 21 na Anambra da aka yi, sakamakon karshe bai bayyana ba
  • Ana iya alakanta hakan da wani korafi da mai mika sakamakon karamar hukumar Orumba ta arewa ya yi inda yace ba a yi zabe a can ba
  • Akwai kuma matsalar karamar hukumar Ihiala wacce aka bayyana za a yi zaben ta a ranar Talata mai zuwa

Anambra - Duk da an tattaro sakamakon zabe a kananan hukumomi 19 daga cikin 21 na jihar Anambra, har yanzu ba a bayyana sakamakon karshe na zaben ba.

Masu kada kuri'a a fadin jihar sun fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar Asabar domin zaben gwamnansu na nan gaba, Daily Trust ta wallafa.

An samu 'yan takara 18 da suka fito neman kujerar a zaben, wanda aka dinga samun matsalar na'urar BVAS da aka yi amfani da ita a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

Da duminsa: INEC ta bayyana zaben Anambra a matsayin 'Inconclusive'

Zaben Anambra: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zabe ba
Zaben Anambra: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zabe ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai, a wurin karbar sakamakon na karshe a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ke Awka, Dr Michael Otu, malami a jami'ar Kalaba wanda ya karbo sakamakon zabe na karamar hukumar Orumba ta arewa, ya ce ba a yi zabe a karamar hukumar ba.

Ya ce tirsasa shi aka yi ya saka hannu kan sakamakon, Daily Trust ta wallafa.

"Na matukar firgita, idan ba don tsarewar Allah ba, da ban kawo yanzu ba. Na fuskanci mummunan lamari a wannan fitar.
“Dan sanda da aka hada mu ya mayar da ni yaron shi. Ko su kallona suka dinga yi kamar dan ta'adda. Har fitsari sai da suka hana ni zuwa. Ban yarda da sakamakon ba, tirsasa ni aka yi na saka hannu," yace.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Yadda aka tirsasawa jami'in INEC sanya hannu kan sakamakon bogi

Ya zargi Comfort Omoruyi, shugabar zaben yankin, da hada wannan al'amarin da kanta.

Amma kuma, EO ta caccaki Otu inda ta zargesa da rashin sanin yadda zai sauke nauyin da ke kansa.

"Ta ce shi farfesan shari'a ne, amma kwata-kwata bashi da hazaka kuma bai san komai ba," tace

Bayan karbar sakamakon, Obi ta bayyana cewa za a yi taro kan halin da aka shiga a karamar hukumar Orumba ta arewa.

Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

A wani labari na daban, akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin jihar da ke Awka a jihar Anambra.

Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zabe a kananan hukumomi sama da biyu bisa uku na jihar, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Asali: Legit.ng

Online view pixel