Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

  • Alamu na nuna cewa jam'iyyar APGA ba ta shirya tattara komatsan ta ba da barin gidan gwamnatin jihar Anambra ba
  • Farfesa Chukwuma Soludo ne a halin yanzu ya ke gaba bayan an bayyana sakamakon zabe a kananan hukumomi 16 na jihar
  • Kamar yadda INEC ta sanar, Soludo ya na da kuri'u 99,765, Ozigbo ya na da kuri'u 44,543 sai Uba da ya ke kuri'u 48,305.

Anambra - Akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin jihar da ke Awka a jihar Anambra.

Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zabe a kananan hukumomi sama da biyu bisa uku na jihar, Daily Trust ta wallafa.

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra
Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra
Asali: Original

Sanata Ifeanyi Uba na jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi nasarar lashe kananan hukumomi daddaya.

A bangaren Sanata Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), har yanzu bai lashe zaben ko karamar hukuma daya ba, Daily Trust ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana jiran sakamakon kananan hukumomi biyu kafin a kammala tare da sanar da sakamakon karshe.

Duk da akwai kananan hukumomi 21 a jihar Anambra, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa ba a yi zabe ba a karamar hukumar Ihiala ta jihar.

A dukkan sakamakon, Soludo ya na da kuri'u 99,765 a kananan hukumomi 16 na jihar, Ozigbo ya na da kuri'u 44,543 sai Uba da ya ke kuri'u 48,305.

Asali: Legit.ng

Online view pixel