Zaben Anambra: Yadda aka tirsasawa jami'in INEC sanya hannu kan sakamakon bogi

Zaben Anambra: Yadda aka tirsasawa jami'in INEC sanya hannu kan sakamakon bogi

  • Jami'in tattara sakamakon zabe ya koka kan yadda yasha wahala a hannun wasu mutane yayin zaben gwamna a jihar Anambra yau Lahadi
  • A gaban jama'a, ya gabatar da sakamakon zabe, amma yace bai amince da sakamakon ba saboda an tilasta masa sanya hannu kan sakamakon bogi
  • Ya shaida cewa, rayuwarsa ta shiga hadari, wannan yasa ya yarda ya sanya hannu kan wani sakamakon da aka bashi a karamar hukumar Orumba

Anambra - Jami’in da ya kawo sakamakon zaben karamar hukumar Orumba ta Arewa, Dr. Michael Otu, ya ba da mamaki a cibiyar tattara zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Lahadi lokacin da ya yi tir da sakamakon da ya sanya wa hannu.

Yace bai yarda da sakamakon ba, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba a yi zabe a Ihiala ba: An dage zaben gwamna a wata karamar hukuma saboda matsala

Ya zargi jami’in zaben da ya kamata ya yi aiki da shi da hada baki da wasu mutane wajen murde sakamakon zabe a yankin.

Zaben Anambra: Jami'i ya ba da mamaki yayin da ya ce bai yarda da sakamakon da ya hada ba
Wurin tattara sakamakon zabe a jihar Anambra | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake mika rahotonsa ga jami’ar da ke kula da masu kada kuri’a a jihar, Farfesa Florence Obi, a wajen tattara sakamakon zabe a hedkwatar INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace babu zabe mai ma'ana a daukacin karamar hukumar.

Ya ce rikicin da ‘yan sanda suka tayar da hankali ne ya sa ya sanya hannu a sakamakon bisa tilas.

A cewarsa:

"Na sanya hannu kan rahoton da ban yi imani da shi ba. Na sanya hannu bisa tilas. An watsamin barkonon tsohuwa. An kulle ni a bandaki, har sai da dan sanda ya fitar da ni.
“Ban iya ko fita don zuwa bayi ba. Sun sa ido sama da kasa. Daga baya, na ga cewa rayuwata tana cikin hadari, don haka, dole na sanya hannu kan sakamakon da suka shirya.

Kara karanta wannan

Rahoto: INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zabe a wasu rumfuna a zaben Anambra

"Na kira abokan aikina na gaya musu cewa ina cikin hadari a nan."

Martanin abokiyar aikinsa

Da take mayar da martani kan batun, wata jami’ar zaben da ba ta bayyana sunanta ba, ta zargi jami’in cewa bai san komai ba game da tattara sakamakon zabe.

A cewarta:

“Wannan mutumin ya fadi abubuwa da yawa a kaina. Amma na lura cewa ba shi da gogewa wajen tattara sakamakon zabe.
“Wannan mutumin bai san hagunsa daga damansa ba. Sakamakon cike yake da kura-kurai. Bai san bambanci tsakanin gudanar da zabe da tattara sakamako ba.

Martanin jami'ar da ke kula da zabe a Anambra

Farfesa Florence Obi, ta ce an gaya mata rikicin da ke faruwa a karamar hukumar.

A cewarta:

“Wannan ita ce karamar hukuma daya tilo da na yi waya da ita, sai da na kira kwamishinan ‘yan sanda na shaida masa cewa rayukan ma’aikatana na cikin hadari."

A halin da ake ciki, ba a bayyana wanda yayi nasara a zaben ba, domin ba a bayyana sakamakon zaben kananan hukumomin Orumba da Ihiala ba.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe sama da 40

Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

A wani labarin, Jam’iyyar APGA ta lallasa jam'iyyar tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, da Sanata Uche Ekwunife, a karamar hukumarsu, This Day ta ruwaito.

Dukansu ‘yan karamar hukumar Anaocha ne, kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Shi ma dai Sanata Victor Umeh ya fito daga karamar hukumar.

Dokta Okene Isaac, malami a Jami’ar Calabar, wanda shi ne jami’in tattara bayanan kananan hukumomi ya ce: “Jimillar masu kada kuri’a 109860, sun amince da kada kuri'u 15940."

Asali: Legit.ng

Online view pixel