Zaben Anambra: Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

Zaben Anambra: Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku

  • Charles Soludo, dan takarar gwamna a zaben 2021 na jihar Anambra ya lashe zabe a karamar hukumarsa
  • Ya lashe zaben ne inda ya kada 'yan hamayyarsa mutum uku da suka fito daga karamar hukuma daya dukkansu
  • Soludo ne dai a gaba-gaba a zaben na gwamna na jihar Anambra, inda ya lashe zabe a mazabu daban-daban

Anambra - Jam’iyyar APGA ta lallasa jam'iyyar tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi, da Sanata Uche Ekwunife, a karamar hukumarsu, This Day ta ruwaito.

Dukansu ‘yan karamar hukumar Anaocha ne, kuma ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne. Shi ma dai Sanata Victor Umeh ya fito daga karamar hukumar.

Da dumi-dumi: Soludo ya lashe karamar hukumar Anaocha, mahaifar 'yan takara uku
Charles Soludo, dan takarar gwamna a jam'iyyar APGA | Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

Dokta Okene Isaac, malami a Jami’ar Calabar, wanda shi ne jami’in tattara bayanan kananan hukumomi ya ce: “Jimillar masu kada kuri’a 109860, sun amince da kada kuri'u 15940."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Manyan jam’iyyun siyasa guda uku da ke da mafi yawan kuri'u su ne:

APC, 2085

APGA, 6911

PDP, 5108

Soludo ne a sahun gaba, APGA ta lashe kananan hukumomi 16 a Anambra

Akwai manyan alamun da ke nuna cewa jam'iyyar All Progressives Grand Alliance ba ta da niyyar tattara komatsanta ta bar gidan gwamnatin jihar da ke Awka a jihar Anambra.

Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan shi ke gaba inda ya lashe zabe a kananan hukumomi sama da biyu bisa uku na jihar, Daily Trust ta wallafa.

Sanata Ifeanyi Uba na jam'iyyar Young Progressives Party (YPP) da Valentine Ozigbo na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi nasarar lashe kananan hukumomi daddaya.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra Jami’in INEC ya tsere da takardun sakamakon zabe sama da 40

A bangaren Sanata Andy Uba na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), har yanzu bai lashe zaben ko karamar hukuma daya ba, Daily Trust ta wallafa.

DG na NYSC ya ziyarci rumfunan zabe, ya yabawa 'yan bautan kasa

A wani labarin, Premium Times ta rahoto cewa, Babban Darakta Janar na kungiyar yi wa kasa hidima (NYSC), Shua’ibu Ibrahim, ya yabawa kishin kasa da ‘yan kungiyar da ke gudanar da aikin zaben gwamna a jihar Anambra.

Mista Ibrahim ya yi wannan yabon ne a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da yake sa ido kan zaben a kananan hukumomi tara na jihar.

Yabon ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NYSC Adenike Adeyemi ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel