Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu

Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu

  • Gwamnonin yankin kudu maso gabas na shirin ganawa da gwamnatin tarayya a kwanan nan
  • A cewar kungiyar gwamnonin, za su tattauna da FG ne a kan lamarin shugaban yan kungiyar awaren IPOB, Nnamdi Kanu
  • Hakazalika za su nemi mafita a kan rikici da sauran kalubale da ke addabar yankinsu bayan samun koken yan kungiyoyin masu fafutuka daba-daban

Kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta bayyana cewa za ta gana da gwamnatin tarayya kwanan nan kan lamarin shugaban yan kungiyar awaren IPOB, Nnamdi Kanu.

Kungiyar ta bayyana cewa ganawar za ta tabbatar da ganin cewa an yi amfani da mafita na siyasa a kan lamarin Kanu wanda ke tsare a hannun rundunar tsaro ta farin kaya, rahoton Punch.

Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu
Gwamnonin kudu maso gabas za su sa labule da Shugaba Buhari kan Nnamdi Kanu Hoto: Mazi Nwonwu
Asali: Facebook

Hakazalika, taron zai magance rikicin da ake fama da shi a yankin kudu maso gabas da kuma dokar zaman gida da kungiyoyin masu fafutuka daban-daban suka kafa, ruwayar Pulse Nigeria.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi ya saki kuma aka gabatarwa da manema labarai a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta ce:

"Muna sane da doka daban-daban da basa bisa ka'ida na zaman gida da kungiyoyin masu fafutuka suka gindaya wa mutanenmu na kudu maso gabas tare da hana su fita duk ranar Litinin da kuma daga 5 zuwa 10 ga Nuwamban 2021.
"Mun gano wasu daga cikin kakakin wadannan kungiyoyin kuma muna ta tattaunawa da su domin hana duk wani na'u'i na rikici da keta doka a kudu maso gabas da bari shugabannin yankin su magance dukkan matsalolin da suka gabatar.
"Don haka muna aiki tare da hukumomin tsaro, jami'an tsaronmu na cikin gida da dukkan shugabanninmu domin kare rayukan mutnenmu da kuma magance dukka lamuran da suka gabatar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

"Muna godiya ga Ohaneze Ndigbo a kan kokarin da suka yi ta kwamitocinsu mabanbanta wajen gabatar da mafita don magance dukkan matsalolin da matasanmu suka gabatar. gwamnonin kudu maso gabas na nazarin rahotanninsu tare da dattawa da shugabannin jihohin yankin kuma ba da jimawaba, za mu gana da gwamnatin tarayyar Najeriya kan lamarin ciki harda amfani da mafitar siyasa a kan lamarin Mazi Nnamdi Kanu wanda muka riga muka fara.
"Muna godiya ga shugabannin addininmu, manyan fastocin kudu maso gabas, sarakunan gargajiya na kudu maso gabas da kungiyar kiristocin Najeriya na kudu maso gabas kan shiga lamarin da suka yi. Za mu yi aiki tare da su don cimma sakamako mai kyau ga mutanenmu da Najeriya."

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

A gefe guda, tsohon hadimin tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Doyin Okupe ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki shugaban IPOB don a samu zaman lafiya a kudu maso gabas bisa ruwayar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

Okupe ya koka a kan yadda gwamnati duk da ganin zubar da jinin da ke aukuwa a jihar amma za ta nuna halin ko-in-kula ta yi zabe a ranar 6 ga watan Nuwamba a jihar.

Ya ce akwai hatsari mai yawan gaske tattare da zaben da za a yi matsawar ba a saki Kanu ba, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel