Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe

  • Tsohon babban hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Dr Doyin Okupe ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan sakin Nnamdi Kanu
  • Ya bukaci gwamnati ta saki Kanu ko za a kawo karshen tashin hankali da rikicin da ke barkewa a yankin kudu maso gabashin Najeriya
  • A cewar sa, sakin shugaban IPOB din ya fi muhimmanci a kan zaben gwamnan jihar Anambra da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba

Anambra - Tsohon hadimin tsohon shugaban kasar Najeriya, Dr Doyin Okupe ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki shugaban IPOB don a samu zaman lafiya a kudu maso gabas bisa ruwayar The Punch.

Okupe ya koka a kan yadda gwamnati duk da ganin zubar da jinin da ke aukuwa a jihar amma za ta nuna halin ko-in-kula ta yi zabe a ranar 6 ga watan Nuwamba a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe
Nnamdi Kanu ya fi zaben Anambra muhimmanci, ku sake shi don a samu zaman lafiya, Doyin Okupe. Hoto daga Punch.com
Asali: UGC

Ya ce akwai hatsari mai yawan gaske tattare da zaben da za a yi matsawar ba a saki Kanu ba, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Punch a Abuja yayin wani taron gangamin jam’iyyar PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Okupe, gwamnatin Jonathan ta yi kokarin ganin ta kashe wutar Boko Haram wacce ta dinga ruruwa, duk da waccan gwamnatin da wannan sun kashe biliyoyin daloli a kan Boko Haram din amma babu wani ci gaba.

Ya ce zaben barazana ne ga harkar tsaro

Kamar yadda ya shaida:

“Babu shakka zaben nan barazana ne ga harkar tsaro, haka ya sa ‘yan Najeriya da dama su ka shiga fargaba. Ko mun ki ko mun so, IPOB ta riga ta yi karfi a yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

“Dole mu yarda da cewa tsarin Biafra ya zo ne don ya zauna. Duk da cewa manyan ginshikan kungiyar matasa ne, su kan su manyan kasar nan fargabar yaki da matasa su ke yi.”

Garba Shehu: Shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin IPOB

A wani labari na daban, Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shari'ar Nnamdi Kanu za ta kawo karshen ta'addancin kungiyar 'yan awaren Indigenous People of Biafra (IPOB).

Ya sanar da hakan ne yayin martani kan caccaka mai zafin da wata jaridar London, The Economist ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daily Trust ta wallafa.

Jaridar ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ta ce mulkinsa ya gaza shawo kan rashawa, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel