Siyasar Najeriya: Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da shugaban jam'iyya saboda abu daya

Siyasar Najeriya: Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da shugaban jam'iyya saboda abu daya

  • Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan reshen jihar Ondo ta dakatar da shugabanta na ƙaramar hukumar Ifedor, Mista Alex Oladimeji
  • Rahotanni sun bayyana cewa mambobin kwamitin zartarwa na karamar hukumar ne suka sa hannun dakatar da shugaban
  • Shugaban APC na jihar, Ade Adetimehin, yace jam'iyyar na zaune lafiya babu wani riikici, kuma zasu shawo kan matsalar Ifedore

Ondo - Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo, ta dakatar shugabanta na ƙaramar hukumar Ifedore, Mista Alex Oladimeji, bisa zarginsa da cin amanar jam'iyya.

Punch ta bayyana cewa matakin dakatarwan na ƙunshe ne a wata wasika mai ɗauke da sa hannun mambobin kwamitin zartarwan APC a yankin.

Shugabannin APC na yankin, sun bayyana ƙarara cewa ayyukan da Oladimeji yake yi kwanan nan sun yi hannun riga da kundin dokokin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Mafi munin mulkin soja da aka taba yi a Najeriya yafi gwamnatin Buhari walwala da jin daɗi, Ortom

Jam'iyyar APC
Siyasar Najeriya: Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da shugaban jam'iyya saboda abu daya Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Meyasa suka dakatar da shugaban?

Wani sashin takardar yace:

"Mu mambobin kwamitin zartarwa na ƙaramar hukumar Ifedore mun dakatar da Alex Akinyemi a yau 3 ga watan Nuwamba, 2021 daga jam'iyyar mu APC."
"Mun ɗauki wannan matakin ne sakamakon ayyukan cin amana da Anti-Party da yake yi wanda ya saba wa kundin dokokin jam'iyya."

Wane irin rikici APC ta faɗa a Ondo?

Shugaban jam'iyyar APC a jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya bayyana cewa babu wani rikici da jam'iyyar APC ke fama da shi a kowane mataki na jihar.

Ya kuma kara da jaddada cewa idan ma akwai wata matsala ta cikin gida a kowace ƙaramar hukuma ce, to APC tana da hanyoyin warware ta.

Yace:

"A halin yanzu da nake magana daku, jam'iyyar APC a jihar Ondo na ɗaya daga cikin reshen dake zaune lafiya a faɗin Najeriya."

Kara karanta wannan

An Fara: Shugaban matasan jam'iyyu biyu da dubbannin mambobi sun koma jam'iyyar PDP

"Muna da hanyoyin warware matsalolin mu na cikin gida a matakin jiha har zuwa gunduma, saboda haka rikicin Ifedore zai zama tarihi."

Duk wani koƙari na jin ta bakin shugaban da aka dakatar ya ci tura, domin wayar salulan shi bata shiga, kamar yadda TVC news ta ruwaito.

A wani labarin kuma Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato, sun hana yan majalisu shiga

Rikici dai yaƙi ci yaƙi cinyewa a majalisar tun bayan tsige kakakin majalisar, Ayuba Abok, tare da maye gurbinsa da Yakubu Sanda.

A halin yanzun babu ɗan majalisar da zai shiga zauren har sai mambobin sun warware matsalolin dake tsakanin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel