Da Duminsa: Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato, sun hana yan majalisu shiga

Da Duminsa: Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato, sun hana yan majalisu shiga

  • Rundunar yan sanda ta ɗauki matakin kwace zauren majalisar dokokin jihar Filato saboda rikicin shugabanci
  • Rikici dai yaƙi ci yaƙi cinyewa a majalisar tun bayan tsige kakakin majalisar, Ayuba Abok, tare da maye gurbinsa da Yakubu Sanda
  • A halin yanzun babu ɗan majalisar da zai shiga zauren har sai mambobin sun warware matsalolin dake tsakanin su

Plateau - Hukumar yan sanda ta ƙwace iko da zauren majalisar dokokin jihar Filato, ta hana kowane ɓangare daga cikin shugabannin majalisan shiga.

Jaridar Punch tace wannan ya biyo bayan rikicin da yaƙi ci yaƙi cinyewa a majalisar kan waye halastaccen shugabanta tsakanin Ayuba Abok, mai wakiltar mazaɓar Jos ta gabas, da kuma sabon wanda aka naɗa bayan tsige wancan, Yakubu Sanda, mai wakiltar mazaɓar Pengana, ƙaramar hukumar Bassa.

Majalisar dokokin Filato
Da Duminsa: Jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato, sun hana yan majalisu shiga
Source: UGC

Wata majiyar yan sandan, ta shaida wa manema labarai cewa mataimakin sufeta, mai kula da shiyya ta 4, wacce ta ƙunshi jihohin Filato, Benuwai da Nasarawa, Mustapha Dandaura, shine ya bada umarni.

Read also

Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ya faru

Bayan ziyarar da ya kai Jos domin gane wa idonsa halin da ake ciki kan Lamarin, AIG ya bada umarnin kwace zauren majalisar baki ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa yan sanda suka ɗauki wannan matakin?

Majiyar da ta tabbatar mana da labarin, ta ƙara da cewa an ɗauki wannan matakin ne domin kaucewa abinda ka iya zuwa ya dawo na karya doka.

Majiyar tace:

"AIG ya kawo ziyara Jos ranar Talata domin ganin halin da ake ciki. Bayan haka ne, yace babban abinda ya dace shine a rufe majalisar dokokin, har zuwa sanda za'a shawo kan lamarin."

Mambobin majalisa sun san da lamarin

Mamba a majalisar dokokin, Timothy Dantong, wanda ya tabbatar da abinda yan sanda suka yi, yace hukumar ta sanar da kowane tsagi matakin da ta ɗauka.

A cewar Dantong, mai wakiltar mazaɓar Riyom:

Read also

Tashin Hankali: Wata Budurwa ta mutu jim kadan bayan ta kwana a dakin saurayinta

"Saboda rikicin dake faruwa, hukumar yan sanda ta ga ya dace ta rufe majalisar dokokin. Mun san AIG ya bada umarni cewa kada ɗan majalisar da ya sake zuwa zauren har sai an sasanta komai."

A wani labarin na daban kuma Babban bututun iskar Gas ya fara kwarara cikin Jama'a a jihar Legas

An samu matsalar kwaranyar iskas Gas daga Bututu a yankin Ikeja jihar Legas, kuma tuni aka shawarci mazauna yankin kada su yi amfani da wuta.

Gas ɗin ya fara kwarara ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Laraba kuma tuni masu kawo agaji daga kamfanin mai NNPC, jami'an kashe wuta na ƙasa da na jihar Legas suka kama hanyar zuwa wurin.

Source: Legit.ng

Online view pixel