Tsohon gwamna ya caccaki APC: Duk APC babu na gari, jam'iyyar 'yan rashawa ce

Tsohon gwamna ya caccaki APC: Duk APC babu na gari, jam'iyyar 'yan rashawa ce

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido bai ji dadin yadda jam'iyyar APC ke tafiyar da al'amuran kasar nan ba
  • Kwanan nan, jigon jam’iyyar na PDP, Lamido ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta gaza wajen gudanar da ayyuka da shugabanci na gari
  • Dan siyasan a yayin da yake tabbatar da halin da al’ummar kasar ke ciki a halin yanzu, ya ci gaba da cewa jam’iyyar juya ce kuma ba ta da abin da zai kawo ci gaba

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya caccaki ayyukan jam’iyyar APC a kasar nan.

Yayin da yake bayyana ayyukan gwamnatin APC kawo yanzu, Lamido ya bayyana jam’iyya mai mulki a matsayin jam’iyya juya wacce ba ta iya samar da kyakkyawan shugabanci ga kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun sauya sheka daga APC zuwa PDP

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jigon na PDP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa, a ranar Talata, 2 ga watan Nuwamba.

Tsohon gwamna ya caccaki APC: Duk APC babu na gari, jam'iyyar 'yan rashawa ce
Tsohon gwamnan jihar Jigawa | Hoto Sule Lamido | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Ya yi nuni da cewa jam’iyyar mai mulki ita ce ke tafiyar da mulki amma ba ta da karfin kawo canjin da ‘yan Najeriya ke bukata.

Lamido ya ce:

“Abin da su (APC) suke cewa PDP kazanta ce amma suna farautar mambobinmu su zo su gina jam’iyyarsu. APC ta ke daukar ‘ya’yan PDP zuwa cikinsu cin rashawa ne.
“Babu nagari a APC. Jam’iyyar ta rashawa matuka.”

Da yake magana kan taron gangamin jam’iyyar PDP da aka kammala da kuma damar da jam’iyyar za ta samu a zaben 2023, Lamido ya bayyana fatan samun nasara ga jam’iyyarsa, inda ya kara da cewa sakamakon taron na nuna hangen ci gaba ga kasar.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya tsorata bayan taron gangamin, ya ce Ayu kalubale ne ga APC

Ya kara da cewa:

"Taron ba taron PDP ba ne, taron gangamin Najeriya ne saboda matsalar rashin tsaro, rarrabuwar kawuna da rashin tattalin arziki a kasar a yau, 'yan Najeriya na fatan samun sauyi."

Ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyar da ke da muradin talakawan Najeriya tun da farko, inda ya kara da cewa manufar jam’iyyar ita ce dawo da fata ga ‘yan Najeriya.

A nasa martanin mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena, ya shaida wa jaridar a wata tattaunawa ta wayar tarho da daddare cewa:

“Za mu kyale PDP su rika hayaniya yayin da muke gudanar da ayyukanmu na karkashin kasa mu ga a nan gaba ko da gaske APC juya ce.
“APC ta haifi ‘yan uku. Mun riga mun haifi gwamnonin su uku (PDP) kuma muna da ciki. Kuma za mu haifi wani nau'i na 'yan uku."

Gwamna ya bayyana shirin PDP, ya ce ta shirya ceto Najeriya daga mummunan shugabanci

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

A wani labarin, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya bayyana cewa, nasarar gudanar da taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya nuna yadda jam’iyyar ke shirin ceto Najeriya daga halin da ake ciki na rashin shugabancin da ya mamaye kasar.

Okowa ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana a shirin gidan talabijin na Channels na "Politics Today" a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba wanda Legit.ng ta sa ido a kai.

Ya ce ‘yan Najeriya sun gaji da tabarbarewar rashin tsaro da na tattalin arziki da ke addabar kasar, inda ya ce PDP ta samu nasarar gudanar da taronta, inda ya aike da sakon da ya dace ga ‘yan Najeriya cewa ya yi daidai da yadda za a canza munanan labari na mulkin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel