Jigon APC ya tsorata bayan taron gangami, ya ce Ayu kalubale ne ga APC

Jigon APC ya tsorata bayan taron gangami, ya ce Ayu kalubale ne ga APC

  • Tun bayan kammala taron gangamin PDP, jam'iyyar APC ta jihar Benue ta yi magana
  • Jigo a jam'iyyar ya ce, zaban Ayu a matsayin shugaban PDP babban kalubale ne ga jam'iyyar APC
  • Ya kuma nemi 'yan APC da su yi aiki tukuru wajen ganin sun kiyaye martabar jam'iyyar a zaben 2023

Benue - Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC reshen jihar Benue, Kwamared Abba Yaro, ya bayyana fitowar Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa a matsayin babban kalubale ga jam’iyyarsa.

Leadership ta ce, yaro ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi a wani taron APC mai taken: “Youth, Politics and Nation Building” a Makurdi babban birnin jihar.

Ayu, tsohon shugaban majalisar dattawa, an zabe shi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa a taron gangamin da ta yi a Abuja ranar Asabar, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

Jigon APC ya bayyana tsoronsa kan sabon shugaban PDP, ya ce Ayu kalubale ne ga APC
Jigon APC a Benue, Kwamared Abba Yero | Hoto: idomavoice.com
Asali: UGC

Yaro ya ce babban kalubale ne ga kowace jam’iyyar siyasa shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya fito daga Benue, ya kuma bukaci matasa da su tashi tsaye domin gudanar da gagarumin aikin da ke gabansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Wannan babban kalubale ne gare mu ganin shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya fito daga Benue. Dole ne mu yi aiki tukuru don samun nasara a 2023. Dole ne mu ajiye duk wani ra'ayi a gefe kuma mu gabatar da 'yan takara masu inganci a zabe mai zuwa. Mu ajiye tunani a gefe mu yi abin da ya dace."

Ya yabawa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi bisa nada matasa a manyan mukamai, inda ya kara da cewa a shekarar 2023 jam’iyyar APC za ta yi hakan a Benue idan har aka ba ta damar mulki.

Kara karanta wannan

Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP

A taron APC na jihar da aka kammala kwanan nan, Yaro yace Comrade Austin Agada shine zababben shugaban jam'iyyar APC na jihar ba kowa ba.

Yaro ya yarda cewa, duk da cewa jam’iyyar ta yanke shawartar ‘yan takara, amma ba a iya cimma hakan ba, aka yi zabe.

Ya ce:

“Eh, an yi kokarin fitar da dan takarar da aka amince da shi, amma ba a yi nasarar hakan ba don haka aka gudanar da zaben kuma Austin Agada ya yi nasara.
"Dukkanmu 'yan uwa ne a APC don haka ya kamata dan uwanmu, Omale Omale ya karbi shan kaye ya jira wani lokaci."

Bayan lashe zabe sabon shugaban PDP ya mika sako ga APC

A wani labarin, Sabon zababben shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya aike da sako ga jam'iyyar APC mai mulki, yana mai cewa “zamu karbe kasar nan.”

Da yake magana da sanyin safiyar Lahadi bayan zaben sa a taron gangamin jam’iyyar na kasa a Abuja, Ayu ya bayyana shirin jam'iyyar na karbe mulkin kasar a zaben 2023, This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC

A cewarsa:

“Nan da makonni biyu za ku ga karfin da zai dawo PDP a kowace jiha. Wasu tsirarun mutane sun yanke shawarar raba Najeriya. Za mu hada kan kasar don ci gaban kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel