2023: Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun sauya sheka daga APC zuwa PDP

2023: Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun sauya sheka daga APC zuwa PDP

  • A ranar Litinin, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari ya ce ba ya da niyyar barin jam’iyyar APC ya koma wata jam’iyya ta daban
  • Abdullahi Abdulkarim-Tsafe, tsohon shugaban ma’aikatan Yari, ya bayyana hakan ta wata takarda a Gusau inda ya ce wallafar da wasu su ka yi akan komawar Yari PDP duk labarin kanzon kurege ne
  • Ya ce duk wadanda su ke wadannan wallafe-wallafen akan sa na jita-jiya a kafafen sada zumunta su na yi ne don zubar ma sa da kimar sa a idon duniya, babu abinda Yari ze yi da PDP

Zamfara -Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari, a ranar Litinin ya ce ba ya da wata niyya ta canja sheka daga jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyyar ta daban, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

Tsohon shugaban ma’aikatan gwamnan, Abdullahi Abdulkarim-Tsafe, ya bayyana hakan bisa ruwayar The Nation ta wata takarda.

Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun ficewa daga jam'iyyar APC
Tsohon Gwamnan Zamfara Yari ya magantu kan batun ficewa daga jam'iyyar APC. Photo credit: Alhaji Salim Yakubu
Asali: Facebook

A cewarsa, duk wasu ma su wallafe-wallafe dangane da komawar tsohon gwamnan zuwa PDP ba gaskiya su ke yadawa ba.

Kamar yadda takardar ta zo:

“Abokai, ‘yan jam’iyya da mutane ma su mana fatan alheri su janyo hankalin mu akan wani labarin kanzon kurege da ya ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani.
“Akwai wasu mutane ma su neman bata mana suna da su ka dinga yada labarai na bogi akan shirin Yari na komawa jam’iyyar PDP.
“Tun asali, babu wani lokaci da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya taba nuna ra’ayin sa akan jam’iyyar PDP.
“Tun farkon siyasar sa, ya fara da jam’iyyar APP, ya koma ANPP, sai APC kuma be taba sha’awar zama dan jam’iyyar PDP ba."

Kara karanta wannan

Guguwar sauya sheka: PDP ta yi babban kamu na wani tsohon minista bayan ya bar APC

Ya ce wajibi ne dakatar da labaran kanzon kurege

Ya kara da cewa:

“Ya zama wajibi mu dakatar da duk wasu labaran kage da su ke tasowa lokaci bayan lokaci.
“Sannan batun cewa tsohon gwamnan ya na ta raba motoci da kudade duk ba gaskiya ba ne.
“Wannan aikin wasu makiya ne da su ke so su zubar da mutuncin sa a idon duniya.”

Ya bayyana cewa duk wadannan karairayin da ake yadawa akan gwamnan ba za su hana shi yin ayyukan da ya yi niyya na ci gaba ba tare da sauran ‘yan APC.

Har ila yau ya bukaci jama’a da su dakata akan yada irin wadannan labaran kuma su dinga tacewa don tantance gaskiya da akasin ta.

Sannan duk da wadannan labaran da ake yadawa akan sa, ba zai hana Yari neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa ba, a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel